1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karfafa dangantaka a tsakanin Amirka da Jamus

July 16, 2021

Shugaba Joe Biden da takwararsa Angela Merkel sun baiyana aniyar aiki tare domin warware duk wasu matsaloli da suka haifar da tsamin dangantaka a tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/3wacv
USA I Angela Merkel und Joe Biden in Washington
Hoto: Susan Walsh/AP/picture alliance

 

Shugabannin sun bayar da tabbacin aiki tare ne da maraicen wannan Alhamis a birnin Washington, lokacin da Shugaba Joe Biden ya karbi bakuncin Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a fadarsa ta White House, Biden ya ce, Amirka tana duba yiwuwar dage takunkumin hana kasashen Turai shigowa kasar da tsohuwar gwamnati ta kakaba a lokacin da annobar corona ta yi kamari. Karin Bayani:  George W Bush ya bayyana wace ce Merkel

Ziyara mai kama da ta bankwana da Angela Merkel ta kawo kafin ta kammala wa’adin mulkinta nan da wasu ‘yan watanni, amma abubuwan da suka tattauna da Shugaba Biden sun hada da batun wani bututun mai da Rasha za ta shimfida domin turo gas zuwa wasu kasashen Turai, wanda Amirka ke adawa da shi. Mai yuwa wannan ziyara za ta sa kasashen na Amirka da Jamus su cimma matsaya ta yadda Rasha ba za ta yi amfani da wannan aikin na bilyoyin daloli domin tsoma baki ko neman tasiri a siyasar wasu kasashen Turai ba. Karin Bayani:  Biden ya yi gyara kan wasu dokoki

Sai kuma batun wasu sojojin Amirka kusan dubu 30 da ke Jamus wanda a lokacin gwamnatin Donald Trump saboda ‘yar-tsama da ya yi da Merkel, ya nemi mayar da dakarun Amirka zuwa kasar Poland, da harkokin ciniki da diplomasiyya tsakanin kasashen biyu. Tun farko da take tsokaci cikin harshen Jamusanci, Angela Merkel ta sake fada karara cewa, Ukraine za ta ci gaba da kasancewa kasar da wannan bututun iskar gas zai bi ta cikinta, kuma za su dauki mataki sosai, muddin Rasha ta ki mutunta tsarin, musanman ganin cewa Ukraine kasa  ce mai ‘yancin kanta. Daga bisani ta sake jinjinawa dasawar da Jamus take yi da Amirka.

Karin Bayani:  Jamus ta zargi Rasha da kutse

Yanzu haka dai, masu sharhi da dama suna jinjinawa tunanin wannan ziyara da Angela Merkel ta kawo, wadda ake ganin kamar dama ce ta dinke barakar da ta dan kunno kai, a tsakanin kasarta da Washington a lokacin tsohuwar gwamnatin Donald Trump.