1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta samu karbuwa a Indonesiya

Suleiman Babayo RGB
September 8, 2022

Kasar Indonesiya ta kasance inda ake nuna goyon baya ga kasar Rasha da Shugaba Vladimir Putin duk da kutsen da ya kaddamar na yaki a kasar Ukraine.

https://p.dw.com/p/4Ga6A
Russland | Wladimir Putin empfängt Joko Widodo
Hoto: Vyacheslav Prokofyev/Sputnik/Pool/REUTERS

Galibin mutane a kasar ta Indonesiya na ganin shugaba Vladimir Putin mai shekaru 69 da haihuwa a matsayin turjiya ga manyan kasashe irin Amirka da suka mamaye lamuran duniya. Ita dai kasar Indonesiya ta yi tir da kutsen da Rasha ta kaddamar kan Ukraine, amma tana gani tukunkumin kasashen duniya bai dace ba.

Dangantaka a tsakanin kasashen biyu ta zama mai daukar hankali ganin yadda cikin wannan shekara Indonesiya ke jagorancin Kungiyar G20 ta kasashen da ke kan gaba wajen karfin tattalin arziki a duniya, kuma a watan Nuwamba mai zuwa kasar za ta dauki bakuncin taron kasashen da zai wakana a tsibirin Bali.

Shi dai tsibirin Bali na Indonesiya ya kasance wajen da 'yan Rasha da dama ke rayuwa da zuwa aiki ko yawon shakatawa. Indonesiya tana da dangantaka mai kyau da Rasha. Akwai bidiyo na goyon bayan Rasha da ake yadawa a kafofin yada labarai na zamani kuma Shugaba Vladimir Putin na Rasha yana da farin jini a wajen 'yan kasar.

Jama'ar kasar na ganin, takaddamar da ake a tsakanin Rasha da kasashen yamma, ya biyo bayan yadda Kungiyar NATO ta kasa cika nata bangaren alkawarin da suka kulla kan izinin shigar da wata kasa a matsayin mamba a kungiyar. Shi ya saka Shugaba Putin na Rasha kaddamar da kutse kan Ukraine. Kasashen Rasha da Indonesiya sun ci gaba da kusantan juna cikin shekarun da suka gabata. Rasha ta goyi bayan samun 'yancin kan Indonesiya a shekarun 1950.

Indonesiya ta kasance kasa mafi yawan musulmai a duniya kuma suna son rayuwa irin na kasashen yammacin duniya da tsarin dimukaradiyya amma suna adawa da tsarin harkokin wajen Amirka.