ECOWAS za ta taimaka kan yaki da ta'addanci
December 6, 2023Wannan kuwa duk da cewa Nijar din na a karkashin takunkumi tattalin arziki da kungiyar ta saka mata tun bayan juyin mulki. Sai dai a yayin da was uke kallon matakin abin yabawa wasu na zargin akwai kanshin cin hanci a ciki. A cikin wani rahotona jadawalin ayyukan kungiyar ta ECOWAS ne wanda shugaban kwamitin gudanarwa na kungiyar ta ECOWAS wato Omar Alieu Touray ya gabatar a gaban majalisar dokokin kungiyar ta CEDEAO a karshen watan da ya gabata, ya sanar da wannan albishir na alkawalin tallafin kudi miliyan daya da dubu 900 na Dalar Amirka kwatankwacin miliyan dubu da 200 na CFA ga kowace daga cikin kasashen uku na Nijar Mali da Burkina Faso.
Karin Bayani: Karar da Jamhuriyra Nijar ta shigar kotun ECOWAS
Sai dai kasancewa tallafin na zama kusan na farko da kungiyar ta yi ga kasashen a lokacin da suke zaman doya da man ja da ita ya sa wasu ‘yan Nijar soma dora ayar tambaya kan manufar da ke tattare da wannan yinkuri na kungiyar ECOWAS. Malam Moutari wani tsohon jami'in hukuma yaki da cin hanci da rashawa a Nijar na ganin akwai kanshin cin hanci a cikin matakin.
Shi ma dai Malam Ibrahim Hamidou dan jarida kana jami'in kula da harkokin sadarwa a fadar firaministan Nijar, cewa ya yi matakin abin yabawa ne amma shi kadai ba zai wadatar ba game da kimar kungiyar ta ECOWAS a idon al'ummomin kasashen. To sai dai wasu ‘yan Nijar na ganin tallafin kungiyar ta ECOWAS ga kasashen uku a wannan lokaci abin yabawa.
Yanzu dai ‘yan Nijar sun zura ido su ga ko wannan tallafin kudi na ECOWAS wata manuniya ce ta yiwuwar fidda wa Nijar takunkumin a taron shugabannin ECOWAS na ranar 10 ga wannan wata ko kuma wani mataki ne na rarrashin ‘yan kasar ta Nijar kafin sake yankewa kasar kauna a taron shugabannin na tafe.