ECOWAS: Nazari kan dalilan juyin mulki a Afirka
October 24, 2023Tun 1975 mulkin dimukuradiyar ke fuskantar koma baya, inda bayanai suka nuna kashi biyu cikin kashi uku na al'ummar duniya na zama a tsari da ba na dimukuradiyya ba. Hankula sun tashi a nahiyar Afrika bayan sake kutsen da sojoji suka yi a wasu kasashen Afrika. A cikin shekaru uku da suka gabata kasashen Afirka shida ne sojojin suka kifar da gwamnatin dimukuradiyya abin da ya nuna koma baya da kuma ya tada hankalin kungiyoyi masu fafutukar kare dimukuradiyya. Kama daga Mali da sojoji suka yi juyin Mulki a 2020 ya zuwa jamhuriyar Nijar a 2023, abin na ci gaba da karuwa. Ambassada Abdulfatah Musa kwashinan kula da harkokin siyasa da tsaro a kungiyar ECOWAS ya ce a nazarinsu ya gano dalilan faruwar haka.
‘'Babban kalubale shine na tafiya tare da kowa a gudanar da harkokin gwamnati bayan an kafa gwamnati, a kasashen Afirka da dama mun ga cewa ko da ana sauya hannun mulki, a tsakanin jamiyyu biyu ne kawai, sannan tsarin mutum guda ya yi kakagida''.
Karin Bayani: Kadawar guguwar sauyi a yammacin Afirka
Akwai dai sauran dalilai da kwararru suka bayyana da suka hada da talauci, rashin tsaro da koma bayan kasashen da aka fsukanci juyin mulki saboda hali na fari. Farfesa Attahiru Jega tsohon shugaban hukumar zabe ta Najeriya ya ce akwai bukatar duba yadda shugabanin siyasa ke gudanar da mulki a Afrika.
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da ya nuna damuwa a kan katsalandan da sojoji ke yi a Afrika ya ce dole ne a hanzarta daukar matakan da suka dace.
‘'Dimukuradiyya na fusknatar kalubale mai yawa a Afrika don haka akwai bukatar tuntubar juna a kan batun tsarin a tafi tare a gudanar da mulki wanda kungiyoyin yankin ya kamata su yi, a karfafa tsarin gudanar da zabe, tattaunawa ta shiga tsakani a kan zaman lafiya da mulki bisa kamanta adalci''
Dr Aisha Laraba Abdullahi tsohuwar kwamishinar kula da harkokin siyasa a kungiyar tarayyar Afirka ta ce akwai bukatar taka tsan-tsan bisa halin da ake ciki.
Duk da wannan kungiyar kasa da kasa ta Idea ta ce har yanzu alummar Afirka na nuna sha'awa ga mulkin dimukurayya duk da cewa tsarin ya gaza yi masu hallaci.