Ghana: Fargaba gabanin babban zabe
September 18, 2024Sanya hannu kan yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya kafin da kuma bayan zabe dai, ya zama wata al'ada a Ghana a duk lokacin da zabe ya karato. Majalisar Zaman Lafiya ta Kasar NPC, na kokarin ganin dukkan jam'iyyu sun amince da wasu bukatu da suka shafi tabbatar da wanzuwar zaman lafiya. Matakin kin sanya hannu kan yarjerjrniyar zaman lafiya da babbar jam'iyyar adawar kasar NDC ta dauka dai, ya bar mutane da dama cikin fargabar ko zaben na bana zai kammala lafiya. Da ya ke magana a kan wannan fargaba da mutane ke nuna wa, shugaban Majalisar Zaman Lafiya ta Kasar NPC Reverend Ernest Adu-Gyamfi ya ce, sanya hannu kan yarjejeniyar abu ne mai muhimmanci wajen dakile tashin hankali yayin zabe. Ya kuma shaida wa kafar yada labarai ta GBC cewa, za su tattauna da bangaren da ya ki sanya hannun. Da yake tattauna da DW wani masanin tsaro a Ghana Kanal Festus Aboagye mai ritaya ya ce, matsalar ta fara ne daga Hukumar Zabe da a cewarsa mutane sun fara dawowa daga rakiyarta. Wannan rashin yarda dai ga dukkan alamu, yana kara yaduwa ko da yake akwai wasu 'yan Ghana da ke ganin sabanin haka.
A nasa bangaren shugaban kungiyoyin da ke sanya ido kan zabuka a Ghana na cikin gida CODEO Albert Arhin ya ce, rashin sanya hannu daga jam'iyyar adawar tamkar bayar da lasisin tayar da zaune tsaye ne. NDC dai ta tsaya kai da fata cewa, Majalisar Tabbatar da Zaman Lafiyar ba ta tabuka abin azo a gani ba a zaben da ya gabata, a dangane da haka ba ta da aminci da ita. A yayin zaben 2020 a kasar kimanin mutane 20 sun rasa rayukansu, kuma takwas daga cikinsu sun rasu ne kan batutuwan da suka danganci siyasa a cewar wata cibiya da ke bin diddigi a Ghana ta Fact Check Ghana. Ita kuwa jam'iyyar da ke mulki NPP a wata sanarwa da babban sakatarenta ya fitar, ta bukaci jam'iyyar adawa ta daina furta kalamai marasa dadi da ke nuna alamun tayar da husuma. NPP ta kuma bukaci dukkan masu ruwa da tsaki su yi tir da matakin kin sanya hannu kan yarjejeniyar ta zaman lafiya kafin da kuma bayan zaben Ghana na bakwai ga watan Disambar wannan shekara. Ana yaba wa kasar Ghana, a matsayin wacce ke gudanar da tsaftatacciyar dimukuradiyya a yammacin Afirka.