NPP ta sahale wa Bawumia takarar shugabancin kasar Ghana
November 5, 2023Bawumia mai shekaru 60, masanin tattalin arziki kuma tsohon ma'aikacin babban bankin Ghana, ya samu sama da kaso 61 na kuri'un da aka jefa a zagaye na biyu na zaben fidda gwani da wakilan jam'iyyar sama da 200,000 daga sassa daban-daban na Ghana suka halarta a wannan Asabar a babban birnin kasar Accra.
Dr Mahamudu Bawumia ya yi nasara ne bayan doke abokan hamayyarsa uku da ke neman takarar shugabancin kasar kamar dan majalisa mai wakiltar Assin Central Kennedy Agyapong da tsohon dan majalisa mai wakiltar Mampong Francis Addi-Nimoh da tsohon ministan noma, Dr Owusu Akoto Afriyie, to amma sai dai karawar ta fi zafi ne a tsakanin Dr Bawumia da dan majalisa mai wakiltar Assin ta tsakiya Kennedy Agyapong.
A yayin jawabinsa bayan samun nasara, dan takarar jam'iyyar NPP ya yi alkawarin inganta tattalin arzikin kasar Ghana da yanzu haka ke a cikin mawuyacin hali.
Bugu da kari ya sha alwashin tafiya da duk wadanda suka fafata a wannan zaben domin ganin jam'iyyarsu ta yi nasara a babban zaben da ke tafe.
Mahamudu Bawumia zai fafata da tsohon shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama wanda babbar jam'iyyar adawa ta National Democratic Congress NDC ta tsayar a matsayin dan takarar ta.