1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceYankin Falasdinu da aka Mamaye

Farin cikin iyalai a Isra'ila da Falasdinu

Mouhamadou Awal Balarabe
January 20, 2025

Farin ciki da annashuwa na ci gaba da mamaye zukatan 'yan Isra'ila da Falasdinawa bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin bangarorin biyu

https://p.dw.com/p/4pO1B
Farin cikin dawowar 'yan Isra'ila da Hamas ta yi garkuwa da su a Gaza
Farin cikin dawowar 'yan Isra'ila da Hamas ta yi garkuwa da su a GazaHoto: Menahem Kahana/AFP

Mutane uku na farko da aka sako a karkashin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas sun hada da Romi Gonen mai shekaru 24 da Emily Damari mai shekaru 28 da Doron Steinbrecher mai shekaru 31. Su wadannan mata sun kasance a hannun Hamas na tsawon watanni 15. Saboda haka ne 'yan uwa da abokan wadanda aka sako suka taru a filin da ake yi wa lakabi da "dandalin garkuwa da mutane" a birnin Tel Aviv don maraba da su da nuna farin ciki. Hasali ma mahaifin Romi Gonen ya shaida wa manema labaran Isra'ila cewa danginta sun shafe sama da sa'o'i 11,000 suna jiran wannan rana.

Karin Bayani: 'Yan Isra'ila uku da Hamas ta sako sun isa gida

Iyalai a Israila na murna da dawowar danginsu da Hamas ta sako
Hoto: Maayan Toaf/GPO/Handout/REUTERS

Mayakan Hamas da suka rufe fuskokinsu ne suka mika mutanen uku ga kungiyar agaji ta Red Cross ta kasa da kasa a wani dandalin da ke birnin Gaza.  Amma bayan da aka mika su ga sojojin Isra'ila, matan uku sun samu damar rungumar iyayensu mata kuma suka yi magana da 'yan'uwansu ta kafar bidiyo a cikin wani hali na murna da dimuwa. Shi kuwa firayiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana farin cikinsa a  lokacin da ya yi jawabi ga wadanda aka sako:

"Na sani, dukanmu mun sani, sun tsallake siradi, sun fito daga duhu zuwa haske. Suna fita daga kangin bauta zuwa 'yanci. Wannan lokacin ya samu ne albarkacin sadaukarwa da gwagwarmayar jarumanmu, jaruman Isra'ila "

Karin Bayani:Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta fara aiki

Falasdinawa na murna da tsagaita wuta tsakanin Israila da Hamas
Falasdinawa na murna da tsagaita wuta tsakanin Israila da HamasHoto: Abed Rahim Khatib/dpa/picture alliance

Ba a Isra'ila kadai ne aka yi bukukuwa ba, a'a, har mazauna zirin Gaza ma ba a bar su a baya ba. Dalili kuwa shi ne: Yarjejeniyar ta sa Isra'ila da Hamas sun tsagaita bude wuta a tsakaninsu, lamarin da ya sa Falasdinawa na zirin Gaza samun sa'ida, a cewar Malak Hussain mai shekaru 21 da ke rayuwa a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat. Baya ma ga matukar godiya ga duk wadanda suka taimaka wajen cimma wannan yarjejeniya, Hussain na fatan samun zaman lafiya mai dorewa.

"A yau ba za a iya misalta tunaninmu ba, ita ce ranar farko ta tsagaita bude wuta, ranar da muka dade muna fata. Babban burinmu shi ne mu koma gidajenmu, mu sake gina rayuwarmu, mu ga Gaza ta zama yadda take a da: wato wurin da za mu sake rayuwa cikin kwanciyar hankali."

Karin Bayani: Isra'ila da Hamas za su musayar fursunoni

Murnar dawowar Falasdinawa da Isra'ila ta sako daga gidan yari
Murnar dawowar Falasdinawa da Isra'ila ta sako daga gidan yariHoto: Ammar Awad/REUTERS

Shi ma Ali Nassar mai shekaru 43, daga Rafah ya yi farin cikin ganin wannan yarjejeniya ta fara aiki:

 "Lokacin da aka sanar da tsagaita bude wuta, na yi matukar farin ciki, wannan yana nufin kawo karshen zubar da jini da ceton rayukan yara. Amma da na dawo Rafah na ga unguwar da nake zaune, sai bakin ciki ya lullube ni, kai ka ce girgizar kasa ta afku, abin da na ganin ya ban tsoro."

Wannan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Hamas ta haddasa rarrabuwar kawuna a gwamnatin Firayiminista Benjamin Netanyahu, lamarin da ya sa ministan 'yan sanda mai tsattsauran ra'ayi Itamar Ben-Gvir da jam'iyyarsa mai ra'ayin kishin kasa suka fice daga kawancen. Su ma wasu ministoci biyu daga jam'iyyarsa sun yi murabus daga mukamansu. Duk da haka, gwamnatin Benjamin Netanyahu har yanzu tana da rinjaye a majalisar dokokin da kujeru 62 cikin 120.

Karin Bayani: Isra'ila da Hamas sun cimma tsagaita wuta a Gaza

Palästinensische Gebiete Beitunia 2025 | Jubel bei Ankunft freigelassener palästinensischer Gefangener
Hoto: Zain Jaafar/AFP

Wannan kashi na farko na yarjejeniyar tsagaita wutar zai dauki tsawon makonni shida ana aiwatar da shi. Hasali ma, Hamas za ta ci gaba da sako ragowar 'yan Isra'ila 30 da ta yi garkuwa da su. A cewar wani jami'in Hamas, za a sake sakin wasu mutane hudu da aka yi garkuwa da su ranar Asabar mai zuwa. Dama dai shugaban Amurka mai barin Joe Biden ya shelanta cewar za a sake sakin wasu mata hudu nan da kwanaki bakwai masu zuwa.

A nata bangaren, Isra'ila za ta saki fursunonin Falasdinawan kusan 1,900 daga gidajen yarin Isra'ila, ciki har da  mata da kananan yara 90, a madadin matan Isra'ila uku da aka sako a ranar Lahadin. An kiyasta cewar kimanin 'yan Isra'ila 95 ne Hamas ke ci gaba da yin garkuwa da su har yanzu a zirin Gaza. Sai dai gwamnatin Isra'ila ta yi imanin cewa kashi daya bisa uku sun riga sun mutu. Wani bangare na yarjejeniyar da Isra'ila da Hamas suka kulla ya tanadi sake ba da damar kai kayan agaji zuwa zirin Gaza. Tuni ma manyan motoci 100 makare da kayan abinci suka kama hanyar shiga Gaza.

Karin Bayani:Adadin mutane da Isra'ila ta kashe a Gaza ya dara dubu 45

Motocin kayan agaji a mashigin Rafah iyaka da Gaza
Motocin kayan agaji a mashigin Rafah iyaka da GazaHoto: Mohamed Abd El Ghany/REUTERS

Yakin da ke tsakanin sassa biyu ya samo asali ne daga mummunan harin da Hamas ta kai wa Isra'ila a ranar 7 ga Oktoban 2023, inda aka kashe mutane 1,200 tare da yin garkuwa da sama da 250. Kungiyar Tarayyar Turai da Amurka da Jamus da sauran kasashe sun ayyana Hamas a matsayin kungiyar ta'addanci. A cewar hukumar lafiya ta Falasdinu da ke karkashin ikon Hamas, sama da mutane 46,000 ne aka kashe a yakin da suke yi da Isra'ila.