1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniAfirka

Olympics: Ko Afirka ta shirya daukar nauyi?

George Okachi MM/SB/LMJ
August 15, 2024

Nahiyar Afirka tana da bunkasa game da harkokin wasanni da zuwa gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya Olympics, amma har zuwa wannan lokaci babu wata kasa daga nahiyar da ta dauki nauyin shirya gasar.

https://p.dw.com/p/4jW3l
Olympics | Afirka | Daukar nauyi
'Yan wasan Afirka, kan taka rawa a gasar wasannin OlympicsHoto: Phil Noble/REUTERS

An shafe shekara da shekaru kasashen Afirka suna halartar gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya na lokacin bazara wato Olympics, inda su kan samu lambobin yabo da ke  daukaka sunan kasashensu a duniya. Yayin da samun lambobin yabo ke karfafa gwiwar 'yan Afirkan, har yanzu da sauran labari ganin babu wata kasa daga nahiyar da ta samu damar daukar nauyin wannan gasa. A wasannin Olympics da aka kammala a birnin Paris na Faransa a wannan shekara ta 2024, babu wata kasa daga nahiyar Afirka da take cikin kasashe mafiya samun lambobin yabo 15 na farko. Kasar Kenya ce kadai ta kasance daga cikin kasashe 30 na farko a jerirn kasashen da suka samu lambobin yabo, inda ta samu nasarar lashe lambobi har 11.

Olympics: Lambobin yabon kasashen Afirka

Akwai masu ganin kafin a kai wannan gaba, tilas kasashen Afirka su zuba kudi wajen inganta kayayyakin more rayuwa da inganta harkokin gwamnati. A shekarar 1995 Afirka ta Kudu ta samu damar daukar nauyin wasan kwallon zari-ruga na duniya kana a shekara ta 2010 ta dauki nauyin wasannin cin kofin kwallon kafa na duniya na FIFA, kuma duk wasannin biyu an yaba da irin shirye-shiryen da kasar ta yi. Sydney Mungala jami'i a Hukumar Kula da Harkokin Wasannin Mata a kasar Zambiya, ya ce tilas kasashen Afirka su ci gaba da yunkurin neman daukar nauyin gasar ta Olympics. Akwai masu tunanin cewa mafarkin kasashen Afirka na daukar nauyin wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniyar ka iya zama gaskiya wata rana, sai dai ana bukatar jajircewar kasashen da kudi wajen bunkasa harkokin wasanni a nahiyar.