1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

INEC: Gurfanar da masu laifin zabe

July 7, 2023

A kokarin wankin suna Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa a Najeriya INEC, ta ce tana shirin gurfanar da dakataccen kwamishinan zaben jihar Adamawa Hudu Ari da wasu mutane da suka tafka laifuka yayin zabe.

https://p.dw.com/p/4TbIf
Najeriya | INEC | Mahmood Yakubu
Shugaban Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa a Najeriya INEC Mahmood YakubuHoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

Kama daga masu sanya idanu a zaben zuwa ga masu adawar Tarayyar Najeriyar dai, ra'ayi ya zo kusan daya kan gazawar hukumar ta INEC. To sai dai kuma daga dukkan alamu hukumar na shirin wankin suna, tare da gurfanar da masu laifuka yayin zabe. Kuma ko bayan dakataccen kwamishinan zabe na jihar Adamawa da INEC din ta ce tana shirin gurfanarwa, hukumar kuma ta ce ta karbi wasu jerin sunaye 215 daga rundunar 'yan sandan kasar da nufin gurfanar da su a kan laifin zaben. Cikin wata sanarwar INEC din dai, Hudu Arin zai fuskanci tuhuma dai-dai har guda shida a wata kotun da za ta zauna a Adamawan. To sai dai kuma daga dukkan alamu, hukumar tana da jan aiki kafin burge masu adawar da suka dauki lokaci suna mata kallon wani bangare na jam'iyyar APC mai Mulki. Arin dai ne jami'in hukumar mafi girma da zai fuskanci hukunci a daukacin tarihin zaben kasar.

Najeriya | INEC |  Zaben 2023
Kokarin INEC na hukunta jami'an da suka aikata laifukan zabeHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

A baya dai yana zama kusan al'ada kammala zabuka a Najeiryar ba tare da kai wa ya zuwa hukuncin da masu sharhi ke kallon na iya sauyin lamura ga kokarin yin sahihin zabe. Faruk BB Faruk na sharhi cikin batun na Siyasa, kuma ya ce sauyin rawa a banagren hukumar na iya tasiri ga makomar zabe cikin kasar. Kokari na ingantar lamura ko kuma hali zanen dutse, ko ya zuwa ina hukumar zaben ke iya kai wa a cikin wankan tsarkin akwai tsoron gaza cimma bukata da ke iya mai da hannun agogo zuwa baya. Hudu Ari dai alal ga misali, ya dauki lokaci yana ikirarin daidai cikin matakin da ya dauka a lokacin zaben Adamawar. Kuma a tunanin Barrister Buhari Yusuf wani lauya mai zaman kansa a Abuja, akwai bukatar taka-tsan-tsan kan takaddamar jihar Adamawar da ma rawar Hudu Arin.