Tinubu: Zai mayar da martani mai zafi kan kisan Sarkin Gobir
August 22, 2024Kama daga talakawa ya zuwa ga masu mulkin Najeriyar dai daga dukka na alamu hankali ya tashi bisa kisan sarkin Gobir da ke a Sokoto Alhaji Muhammad Bawa. Makonni kusan uku da suka gabata ne dai wasu da ake jin 'yan fashin daji ne suka kame basaraken suka kuma nemi kudaden fansa.Wani fefen bidiyo a cikin mako na jiya ne dai ya fara tada hankali cikin kasar yayin da maragayin ke rokon dauki da nufin cetonsa, amma a yanayi maras kyau sosai.
To sai daikuma labarin na hallakashi dai ya jawo damuwa da girman gaske a cikin Najeriya in da shugabanni na kasar suke alkawarin ramuwa irin ta gayar-gaya. Wata sanarwar fadar gwamnatin kasar dai ta ce shugaba Tinubu ya kadu sosai da kisan da ya ce yana zaman na mugunta. Shugaban kuma a fadar kakakinsa ya sha alwashin mayar da martani mai zafi da nufin aike sako a fadar Abdul Aziz Abdul Aziz da ke zaman daya a cikin kakaki na shugaban: '' Hankali na shugabanni shi kansa shugaban kasa da mukarabbansa ya tashi kwarai da gaske, musamman ma ganin yadda aka yi ta kokari amma wadannan 'yan ta'adda sai da suka aiwatar da wannan mummunan aiki.''
Kuma kamar yadda shugaban kasa ya fadi, lallai-lallai dole a dauki mataki kan wadannan mutane ta yadda ran sarkin Gobir bai tafi a banza ba. In Allah ya yarda gwamnati za ta dauki kwakwaran mataki kan wadanda suka aikata wannan laifi domin zama izina ga masu irin wannan mummunar manufa. To sai dai kuma kama daga shugaba Jonathan zuwa ga Buhari, ko bayan Tinubun da ke bisa mulki yanzu, ya kasar dai sun saba da kalamai da ke nuna alamun taunin tsakuwa, don bai wa ayya tsoro.Yahuza Getso dai na sharhi cikin batun rashin tsaron, kuma ya ce da siyasa cikin rikicin da ke gabashin na Sokoto.