1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tura sojoji jahohi magance matsalolin tsaro a Najeriya

August 20, 2024

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta jibge sojoji a cikin gonaki domin kare lafiyar manoma a yankin arewa maso yammaci da arewa maso gabas na kasar.

https://p.dw.com/p/4jhoB
Najeriya Kankara | Jami'an tsaro a jihar Katsina
Jami'an tsraon NajeriyaHoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

Rundunar sojan Najeriya ta sanar da tura jami'anta a wasu jahohin arewacin kasar domin bai wa manoma kariya a gonakinsu domin su samu su yi noma sakamokon yadda 'yan bindiga ke hana su zuwa gonakin abin da ya sa al'ummar yankunan da aka ce an tura jami'an tsaron ci gaba da martani. Daraktan hulda da manema labaru na rundunar Manjo Janar Edward Buba ne ya tabbatar wa DW tura dakarun a wani matakin da zai bai wa manoma da yawa dama noma gonakinsu tun daga yanzu har zuwa lokacin girbi.

Karin Bayani: 'Yan bindiga sun sace mutane 150 a Zamfara

Najeriya | Manomi a Najeriya
Manomi a NajeriyaHoto: imago/Aurora Photos/Peter Essick

Jihar katsina na daga cikin jahohin da aka ce an tura dakarun shin mutanan da ke yankunan da 'yan bindiga suka addaba za su ce? Inda wasu mazauna garuruwan suka ce ba su ga sojojin ba tukunna. Jihar Zamfara tana daga cikin jahohin da hare-haren 'yan bindigar ya yi kamari su ma DW nemi sanin albarkacin bakin wasu al'umma ko sun fara zuwa gonakinsu sakamokon tura karin sojojin kuma a yankin karamar hukumar Tsafe kawo wannan lokaci babu batun ganin sojojin.

Sakamakon bayanan wannan al'umma na jahohin Katsina da Zamfara DW ta sake waiwayar Manjo Janar Bubu to me ya faru al'ummar ba su fara ganin wani canji ba? Inda ya bayyana cewa zai dauki lokaci wajen tsara dabaru da turo sojojin daga kwamandodjin da ke kula da yankunan. Masana dai na cewa harkokin noma da kiwo a arewacin Najeriya sun samu gagarumun koma-baya saboda yadda 'yan bindiga suka dade suna gallaza wa manoma kama daga garkuwa da su dan amsar kudin fansa da kuma sanya masu haraji.