1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Harris ta sa Trump kare kansa a zazzafar muhawara

September 11, 2024

Kididdigar jin ra'ayin jama'a ta nunar cewar 'yar takartar Democrats Kamala Harris ta samu rinjaye a kan Donald Trump na Republican. Sai dai manazarta na ganin cewar da yawu muhawarar ta sauya tunanin masu zabe.

https://p.dw.com/p/4kVVh
Dubban Amurkawa sun kalli muhawara tsakanin Harris da Trump a kafar talabijin
Dubban Amurkawa sun kalli muhawara tsakanin Harris da Trump a kafar talabijinHoto: Mario Tama/Getty Images

Bayan da mijinta ya mika mata amsa-kowar magana, mataimakiyar shugaban Amurka kuma ‘yar takarar shugabancin kasar a jam'iyyar Democrats Kamala Harris, ta yi dirar mikiya kan abokin hamayyarta Mr. Trump, inda ta ce ba shi da abin da zai ce wa Amurkawa sama da miliyan 81 da suka katse masa mafarkin tazarce a zaben da ya gabata. Shi ma Trump bai yi kasa a gwawi ba wajen mayar da mata kakkausar martani dangane da manufofinta kan tattalin arziki da ‘yan gudun hijra da inshorar iyali da dai sauran batutuwan da suka shafi manufofin Amurka kan kasashen ketare.

Karin bayani:An fara zaben wuri a Amurka 

Masana irin su Laura Merrifield Wilson, ta sashen koyar da kimiyyar siyasa a Jami‘ar Indianapolis ke cewa babu wani abu da muhawarar za ta canza dangane da dabi'ar masu kada kuri'a.Ta ce: " Mun ga yadda Harris ta samu tagomashi kan abokin hamayyarta duk da cewa akwai kura-kurai da kuma batun yadda ake kambamata. amma akwai hasashen komawa kan gwadabe bayan karkare muhawarar. Ta la'akari da abin da yake kasa, Harris ta taka rawar gani a wannan muhawara.”

Me muhawara za ta sauya a takarar Trump da Harris?

Muhawara ta yi zafi tsakanin Trump da Harris a Amurka
Muhawara ta yi zafi tsakanin Trump da Harris a AmurkaHoto: Alex Brandon/AP/picture alliance

Dan takarar shugabancin kasar a karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump, ya soki manufofin gwamnatin Biden kan bakin haure, inda ya ce miliyoyin mutane na shigowa Amurka daga gidajen yari da gidajen masu lalurar kwakwalwa da masu neman mafaka daga kasashe daban-daban da shigowarsu ke haifar da gibi wajen ayyukan yi.

Karin bayani:Kalubalen da ke gaban Kamala a Amurka

Shugaban ofishin DW da ke birnin Washington na Amurka ta ce ba wa Harris nasara a murawarar ba zai sauya biyayyar da magoya bayan Trump ke masa ba. Ta kara da cewa: " Lamarin zaben Amurka na 2024 ba zai fayyace gaskiya ba dangane da batun zaben cancanta, ba na tunanin rabin kuri'un Amurkawa zai tsaya a kan manufa ta akida. Magoya bayan Trump za su ci gaba da kasancewa da shi. Magoya bayan Harris za su fi zakewa wajen kasancewa da ita biyo bayan bajintar da ta nuna"

Ya kasashen duniya suka kalli muhawarar Harris da Trump?

Wane ne zai shiga fadar White House tsakananin Harris da Trump bayan zaben 2024?
Wane ne zai shiga fadar White House tsakananin Harris da Trump bayan zaben 2024?Hoto: Olin Dozier/NurPhoto/picture alliance

Muhawarar ta mintuna 50 ta sa ‘yar takarar shugabancin Amurka a jam'iyyar Democrats Kamala Harris da abokin hamayyarta na jam'iyyar Republican Donald Trump sun yi gaba da gaba gabanin babban zaben shugaban kasar a watan Nuwamban 2024. Wannan ya sanya kasashen duniya da dama tofa albarkacinsu kan buwayar dimukuradiyyar Amurka duk da cewa kasashe irin su Rasha sun barranta kansu daga bibiyar muhawarar da 'yan takarar ta Amurka suka tafka.

Karin bayani:Trump: Babu ja da baya wajen korar baki idan na lashe zabe

Mai Magana da yawun fadar Kremlin ke nan Dmitry Peskov ya ce Rasha ba za ta yi shiga shirgin muhawarar Amurka ba, hasali ma ta haramta wa kanta kallon muhawarar. Wannan gaba da gaba ta kasance abin tattaunawa a da'irar siyasar duniya musamman ga masu bibiyar siyasar Amurka da kuma rawar da Amurka ke takawa a Gabas ta Tsakiya da kuma yakin Gaza har ma da yakin Rasha da Ukraine.