Isra'ila ta ba da sa'o'i 24 don kwashe mazauna Gaza
October 13, 2023Wannan na nuni da shirin tabbatar da alwashin da Isra'ila ta dauka na abkawa Zirin Gaza domin fatattakar 'yan kungiyar Hamas da ta kira a matsayin 'yan ta'adda tare kuma da kwato mutanen da ta yi karkuwa da su lokacin da aka fara rikicin.
Karin bayani: Kokarin sako Isra'ilawa daga hannun Hamas
Sai dai a lokacin da ya ke sanar da wannan umurni na Isra'ila, kakakin sakataren Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ya bukaci Tel-Aviv da ta soke wannan mataki yana mai gargadin kadda bayan kashe-kashen da aka yi a kasa da mako guda, yankin ya sake fadawa cikin munmunan yanayi.
Karin bayani: Isra'ila ta yi wa yankin Gaza kawanya
Daga nasa waje jakadan Isra'ila a Majalisar Dinkin Duniya Gilad Erdan tir ya yi da wannan martani da majalisar ta yi yana mai zarginta da rufe idanuwa a lokacin da ya ce kungiyar Hamas ke cefano makamai tana boyewa a Zirin na Gaza.
A wannan Jumma'a (13.10.2023) kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai yi taron gaggawa a asirce kan wannan sabon rikici na Isra'ila da kungiyar Hamas yayin da ake daf da cika mako guda da barkewarsa.