1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman makoki a Jamhuriyar Nijar

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 26, 2020

Fadar shugaban kasar Jamhuriyar Nijar ta gudanar da taron karrama marigayi tsohon shugaban ksar Tandja Mamadou wanda Allah ya yi wa rasuwa a ranar Talatar da ta gabata bayan ya yi fama da rashin lafiya.

https://p.dw.com/p/3ls6E
Niger Niamey Ex-Präsident Tandja Mamadou
Marigayi tsohon shugaban kasar Nijar Tandja MamadouHoto: DW/M. Kanta

Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar ta Nijar ne ya jagoranci karrama tsohon shugaban kasar, gabanin jana'izarsa a garin Maine Soroa a cikin jihar Diffa, inda aka gudanar da addu'o'i da kuma taken kasar. Taron ya samu halartar manyan jami'an gwamnatin kasar da suka hadar da ministoci da ‘'yan majalisa da kuma sauran 'yan uwa da aminnan marigayin, har ma da tsohon shugaban kasar Alhaji Mahaman Ousmane. 

Al'ummar ta Jamhuriyar Nijar dai, na cikin alhinin rasuwar ta Tandja da suke bayyanawa da cewa babban rashi ne ga al'ummar Nijar baki daya. Ba ma dai al'ummar ta Nijar ne kadai ke jimamin rasuwar Tandja ba, har ma da sauran kasashen Afirka musamman ma Najeriya, inda Na jeriyar ta nunar da cewa  za a dade ana tuna shi a daukacin yankin na yammacin Afirka baki daya. 

Al'ummar ta Jamhuriyar Nijar da dama dai na kallon Tandja Mamadou a matsayin jarimin shugaba kuma dan kishin kasa, duk da cewa wasu na ganin ya so ya wuce makadi da rawa bayan da ya yi tazarce, abin kuma da ya yi sanadiyyar da sojojin kasar suka yi masa juyin mulki.