1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus: Manufofin kan neman mafaka

Usman Shehu Usman
November 7, 2023

Kasar Jamus na son karfafa manufofinta na neman mafaka. Matakan sun hada da samar da katin biyan kudi maimakon bayar da tsabar kudi.

https://p.dw.com/p/4YWcr
Berlin Bund-Länder-Treffen im Bundeskanzleramt
Hoto: Bernd von Jutrczenka/dpa/picture alliance

Bisa ga tsarin da ake aiki da shi a baya, shi ne duk mai neman mafakar siyasaidan ya zauna a Jamus tsawon watamnni 18, to yana da yancin samun tallafin bukatun yau da kullum, amma yanzu sai mai neman mafaka ya yi shekaru uku kafin ya samu wannan damar. A tsawon shekaru uku za a rika bashi Euro 410 wadanda daga cik za a yi lissafin abincin da zai ci da kudin hayan wurin kwana. A lokacin da yake magana bayan taro da gwamnonin jihohin Jamus 16, Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya fada cewa wannan matakin abun tarihi ne aka cimma, kan batun neman mafaka Jamus.

Berlin  Auftaktbilder Bund-Länder-Gipfel im Bundeskanzleramt
Hoto: Political-Moments/IMAGO

"Mun san cewa akwai mutane da yawa da ke zuwa Jamus kuma suna neman mafaka a nan. Ba duka ne za su iya zama ba saboda akwai masu yin hijira da yawa ba bisa ka'ida ba wadanda ke isa Turai da Jamus. Manufarmu daya ita ce sauya wannan lamarin. Don haka mun kulla yarjejeniyoyin da suka dace, wadanda a yanzu muke aiwatar da su ta hanyar doka, a duk matakan da ke karkashin alhakinmu."

Karin Bayani: EU: Masalaha kan 'yan gudun hijira

Daga cikin matakan da gwamnatin Jamus ta cimma sun hada da karfafa binciken kan iyakokin kasar na tsawon lokaci. Gwamnatin Tarayyar Jamus za ta yi haka ne bisa hadin kan kasashe da ke iyakoki da su. Kasashen su ne Switzerland, Ostiriya, Poland da Jamhuriyar Cek. Wannan batun da ya shafi masu neman shigowa ke nan.

Amma ga Niklas Hader da ke Cibiyar hadin kai da binciken kan yan gudun hijira a kasar da keBerlin ya ce biyan masu neman mafakar siyasar alawus ta kati na musamman maimkon kudi a hannu, yana tattare da kalubale.

Yan gudun hijira da suka shigo ta tsibirin Canary Island a kasar Spain
Yan gudun hijira da suka shigo ta tsibirin Canary Island a kasar SpainHoto: H.Bilbao/Europa Press/ABACA/picture alliance

"An gwada ka'idar hakan da kuma fa'ida yin hakan tun a cikin shekarun 1990, Haka kuma an sake gwada tsarin a shakarar 2015, kuma ya tabbatar da cewa biyan kudi ta katin bai da wani amfani."

Karin Bayani: EU ta jingine tattaunawa kan mafakar siyasa

Abind a ke rubuce a kundin tzsarin mulkin Jamus shi ne, duk sabon dan gudun hijira dole a rika biyansa Euro 150 kudin kashewa baya ga saurarn alawus na wajen kwana da kuma abinci. Amma yanzu abinda jihohi da gwamntin Tarayyar Jamus suka cimma shi ne, duk dan gudun hijira za a rika ware masa Euro 7500 a shekara, to amma ga masana ko da shi a zahiri gwamnatin Jamus za ta yi tsimin kudi, amma ga ‘yan gudun hijira a ce su biya haya su sayi abinci da sauran bukatun yau da kullum duk a cikin wannan kudi, to babu inda zai kai domin ya yi matukar kasawa