1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTanzaniya

Jamus ta roki gafara kan kisan lokacin mulkin mallaka

November 1, 2023

A ci gaba da ziyarar da yake a nahiyar Afrika Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya nemi gafara a gurin mahukutan kasar Tanzaniya kan laifukan da kasarsa ta aikata a lokacin mulkin mallaka.

https://p.dw.com/p/4YHfx
Jamus ta roki gafara kan kisan kiyashi a Tanzaniya
Frank-Walter Steinmeier shugaban kasar Jamus lokacin ziyara a TanzaniyaHoto: Bernd von Jutrczenka/dpa/picture alliance

Shugaba Frank-Walter Steinmeier ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci wani gidan adana kayan tarihi da ake kira Maji-Maji da ke birnin Songea na Kudancin Tanzaniya inda bayan ya nuna alhini ya ce: ''Ina neman gafara kan abin da Jamusawa suka aikata lokacin kakannin 'yan wannan kasa da ke gabashin Afrika''.

Karin bayani: Aiwatar da yarjejeniyar Jamus da Namibiya

Frank-Walter Steinmeier shugaban kasar Jamus lokacin ziyara a Tanzaniya
Frank-Walter Steinmeier shugaban kasar Jamus lokacin ziyara a TanzaniyaHoto: Bernd von Jutrczenka/dpa/picture alliance

A yayin wannan ziyarar dai Mr. Steinmeier ya gana da zuriyar Cif Songea Mbano, jagoran 'yan tawaye na wacan lokaci, wanda Jamusawa suka rataye tare da fille kawunansu da shi da wasu mayakansa 66.

Masana sun yi kiyasin cewa an kashe mutanen da yawansu ya kai dubu 200 zuwa dubu 300 na al'ummar Tanzaniya a lokacin wani bore na adawa da mulkin mallaka da ake kira "Maji Maji Rebellion" wanda aka yi tsakanin shekarun 1905 zuwa 1907.