1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta yanke kauna da Nijar

July 17, 2024

Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock ta ce Jamus ba za ta ci-gaba da kulla alaka da Nijar ba saboda rashin yardar da ta shiga tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/4iOUG
Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock da Alassane Ouattara na kasar Côte d'Ivoire
Hoto: Britta Pedersen/dpa/picture alliance

Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock ta ce Jamus ba za ta ci-gaba da kulla alaka da Jamhuriyar Nijar ba saboda rashin yardar da ta shiga tsakaninsu da majalisar mulkin sojin kasar. Baerbock ta bayyana hakan ne a lokacin da take ganawa da Shugaba Alassane Ouattara na kasar Côte d'Ivoire a ziyarar da take yi a yankin yammacin Afirka.

Baerbock ta kara da cewa: "Duk da rashin aminci tsakanin bangarorin biyu, Jamus ba za ta dakatar da tallafin jin kai da take bai wa al'ummar Nijar saboda ba, su da hannu cikin abun da ya faru."

Karin bayani: Baerbock tana ziyarar kasashen Senegal da Cote d'Ivoire

Tun dai a ranar 6 ga wannan watan da muke ciki ne, Jamus ta sanar da kawo karshen ayyukanta a sansanin sojin saman Nijar da ma kamalla janye sauran gomman dakarunta zuwa nan da ranar 31 ga watan Agusta.

Tun bayan da Nijar ta fuskanci juyin mulki a bara, sojojin da ke mulki suka yanke hulda da tsohuwar uwargijiyar kasar, Faransa da ma sauran kasashen yammacin Turai, inda suka fara dasawa da Rasha.