1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jaridun Jamus: Matsayar Afirka kan rikicin Isra'ila da Hamas

Abdullahi Tanko Bala MAB
October 27, 2023

Jaridar die tageszeitung a sharhinta mai taken rarrabuwar kawuna a Afirka ta ce kasashen Kenya da Kwango na goyon bayan Isra'ila yayin da Afirka ta Kudu ke jaddada goyon bayanta ga Falasdinawa.

https://p.dw.com/p/4Y6wg
Kenya na cikin jerin kasashen Afirka da ke goyon bayan Isra'ila a rikicinta da Hamas
Kenya na cikin jerin kasashen Afirka da ke goyon bayan Isra'ila a rikicinta da Hamas

((die tageszeitung 

 

Jaridar die tageszeitung ta ce Kowa na nesa kansa da ta'addanci, wannan shi ne yadda Afirka ke tattauna sabon yakin da ya barke a Gabas ta Tsakiya. Yayin da Kungiyar Tarayyar Afirka AU ke kallon batun Israila da Hamas da kyakkyawar manufa, a waje guda ta tsaya tsaka-tsaki ba tare da daukar bangare ba. Shugaban hukumar AU Moussa Faki Mahamat ya yi roko ga gangarorin biyu tun lokacin da Hamas ta kai hari kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba da cewa su tsagaita wuta a kai zuciya nesa a kuma tattauna ba tare da wani sharadi ba, don komawa kan masalahar samar da kasashe biyu na Isra'ila da Falasdinawa da za su zauna lafiya daura da juna cikin girma da arziki.

Karin bayani: Jaridun Jamus: Yanayin Gaza ya ja hankalin jaridun Jamus

Ya ce hana al'ummar Falasdinawa 'yancin kafa kasarsu shi ne tushen rikicin da ake samu akai akai. Shugaban na hukumar Kungiyar Tarayyar Afirka ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa musamman manyan kasashen duniya masu karfin fada a ji da su dauki nauyin tabbatar da zaman lafiya da kuma tabbatar da hakkin al'ummar kowane bangare.

Firaministan Isra'ila Netanyahu na da kyakkyawar alaka da wasu kasashen Afirka
Firaministan Isra'ila Netanyahu na da kyakkyawar alaka da wasu kasashen AfirkaHoto: picture-alliance/AP Photo/M. Ayene

Tun bayan barkewar rikicin yankin Gabas ta Tsakiya, kasashen Afirka da dama suka bi sahun wasu kasashen duniya wajen jajantawa da kuma nuna goyon baya ga Israila , wadanda suka hada da Ghana da Kenya da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da kuma Ruwanda inda suka fito karara suka yi Allah wadai da ta'addanci da kuma hari kan fararen hula wadanda ba su ji ba ba su gani ba a cewar shugaban Kenya William Ruto. Sai dai kuma wasu 'yan siyasa a Kenya sun soki lamirin jawabinsa inda suka yi kiran katse huldar dangantaka da Isra'ila. A Najeriya kasa mafi yawan jama'a a Afirka kuwa, shugabanta Bola Ahmed Tinubu kira ya yi ga Israila da Falasdinawa su zauna su tattauna su kuma dauki batun sulhu da matukar muhimmanci.

Shugabannin EU da dama ne suka hada gwiwa da Tunisiya don yaki da bakin haure
Shugabannin EU da dama ne suka hada gwiwa da Tunisiya don yaki da bakin haureHoto: Freek van den Bergh/ANP/picture alliance

  Yarjejeniyar Eu da Tunisiya kan hijira ta ci tura

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung, tsokaci ta yi a kan yarjejeniya da ta shafi 'yan gudun hijira tsakanin Tunisiya da Kungiyar Tarayyar Turai. Dama shugaban Tunisiya Ka'is Saied ya yi watsi da tayin Kungiyar Tarayyar Turai na tallafin Euro miliyan 60 domin dakile kwararar 'yan gudun hijira zuwa kasashen Turai. Sai dai kuma idan babu tallafi daga waje tattalin arzikin kasar na iya durkushewa.

Karin bayani: Yarjejeniyar EU da Tunisiya kan 'yan gudun hijira

Jaridar ta ce duk wanda zai magana game da 'yan gudun hijira a Tunisiya, sai ya yi maganar kudi daga Kungiyar Tarayyar Turai ko kuma daga Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF. Haka ma takaddamar da ke tsakanin Tunisiya da Kungiyar Tarayyar Turai a Brussels a kan kudi ne. EU  na fuskantar matsin lamba daga gwamnatin ra'ayin rikau ta Giorgia Meloni ta Italiya kan 'yan gudun hijirar da ke kwarara zuwa Turai a kan teku ta Tunisiya. Yanzu dai yarjejeniya ta ci tura tsakanin Tunisia da Kungiyar Tarayyar Turai, abin da ke nuna rashin jituwa a muradun bangarorin biyu.

Najeriya ta samu galaba a kan  jami'an kamfanin P&ID a katu saboda bada cin hanci
Najeriya ta samu galaba a kan jami'an kamfanin P&ID a katu saboda bada cin hanci Hoto: Leonid Altman/Zoonar/picture alliance

Shari'ar Najeriya da kanfanin P&ID ta dauki hankali

Najeriya ta yi nasara a gagarumar shari'ar zamba a London, shi ne taken sharhin jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung. Jaridar ta ce kotu ta kori karar biliyoyin daloli na kamfanin makamashin Gas wanda ka iya jefa Najeriya cikin damuwa ta fuskar tattalinn arziki da harkokin kudade. Jaridar ta ce bayan tsawon shekaru ana dambarwar shari'a, kasar ta yammacin Afirka ta yi nasarar tsallake siradi na biyan dala miliyan 11 bayan da alkalin babbar kotun ta London ya yi watsi da karar a hukuncin da ya yanke.

Karin bayani: Kamfanin Shell zai biya manoman Najeriya diyya

Mai shari'a Robin Knowles ya yanke hukuncin cewa jami'an kamfanin P&ID sun bada cin hanci ga ma'aikatar mai ta Najeriya a kwangilar makamashin gas tsakaninsa da Najeriya a shekarar 2010. Sai dai kamfanin na P&ID har yanzu yana da damar daukaka kara.

Hukuncin kotun London ta dadada ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Hukuncin kotun London ta dadada ran Shugaba Bola Ahmed TinubuHoto: Sunday Aghaeze/AP Photo/picture alliance

Ga shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, hukuncin tuntuben dadin gushi ne wanda ya zo a daidai lokacin da ya samu nasara a cikin gida, inda kotun koli ta tabbatar da shi a matsayin shugaban kasa a karar da manyan abokan hamayyarsa biyu suka shigar a gabanta.

Najeriya da ke zama kasa mafi karfin aziki a Afirka na fama da dumbin bashi da tsadar rayuwa da kuma tashin gwauron zabi na farashin kayayyaki da ya haura kashi 25%.