Sahel: Sojoji sun gaza hana rashin tsaro
October 16, 2023A birnin Bamako fadar gwamnatin kasar Mali dai abubuwa suna tafiya cikin tsanaki, amma akwai abin da ake gani zai iya sauya al'amura sakamakon zanga-zangar lumana da malamin addinin Islama mai karfin fada aji Imam Mahmoud Dicko ya kira kan jinkirta zaben da sojoji suka yi. Tuni wata kungiya ta kusa da malamain ta nuna adawa da zanga-zangar, abin da ke nuna yiwuwar samun taho-mu-gama tsakanin bangarorin da suke kawance. Gwamnatin mulkin sojan Mali karkashin jagorancin Assimi Goita da ke tunkarar shekaru uku kan madafun iko, tana ci gaba da rasa goyon bayan da take da shi tsakanin al'umma sakamakon jinkirta zaben da kuma matsalolin tsaro. Al'amura sun sauya daga shekara ta 2021 a kasashe makwabtan Malin lokacin da Goita ya kwace madafun iko, inda kasashen Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar suka shiga rukunin da aka yi juyin mulkin. Gabanin juyin mulkin na Jamhuriyar Nijar dai, kasashen Yamamcin Duniya suna dasawa da Shugaba Mohamed Bazoum da sojoji karkashin jagorancin Abdourahamane Tiani suka kifar a watan Yuli.
Sojojin kasashen da suka kwace madafun ikon dai na samun goyon bayan mutane sai dai akwai gagarumin kalubale musamman na rashin tsaro, inda 'yan ta'adda ke cin karensu babu babbaka a wasu yankunan kasashen. Lompo Alassane na kungiyoyin fararen hula a Burkina Faso, ya ce cikin kwanakin da suka gabata mayaka kimanin 500 dauke da makamai sun kaddamar da farmaki kusa da daya daga cikin manyan birane mai iyaka da Mali amma sojoji da 'yan sa-kai sun dakile farmakin da aka samu rasa rayuka daga duka bangarorin. Yankin na Sahel ya dade karkashin tarnakin tsaron, kuma jim kadan bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar aka fara neman sojojin Faransa su fice daga kasar gami da zanga-zangar kin jinin Faransan. Moussa Tchangari na kungiyar farar hula ta Alternative Espaces Citoyens da ke Jamhuriyar ta Nijar ya tabbatar da cewa babu sauyin yanayin tsaro da aka samu, domin haka sojojin ba su da mafita mafitar siyasa ake bukata. A kasar Mali ma dai, tun bayan janyewar Faransan lamura ba su inganta ba.