Kokarin ceto daliban da aka sace a Kaduna
March 8, 2024Kimanin yara 300 ne dai 'yan bindigar suka sace daga makarantunsu, tare da yin awon gaba da su a kan babura. Tuni dai gwamnatin jihar Kadunan ta baza jami'an tsaro a daukacin dajin da ke kewaye da yankin na Kuriga da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, domin ceto wadannan yara. Wannan dai shi ne sacta da kuma garkuwa da daliban na baya-bayan nan da ya afku a Kadunan, lamarin kuma da masu fafutuka ke dora alhakin faruwarsa a kan gawzawa ta fannin tattara bayanan sirri da kuma matsalar kai dauki a makare daga jami'an tsaro.
Tuni dai shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu ya yi tir da faruwar lamarin, cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin kasar ta fitar. Sanarwar ta nunar da cewa Tinibu ya ce ya samu bayanai daga jami'an tsaro kan satar dalibai a jihohin Kaduna da Borno, wanda ya ce ya bayar da ummurni da a gaggauta ceton su. Tinubun ya kuma ya janjantawa iyalan wadanda abin ya shafa, yana mai ba su tabbacin cewar nan ba da jimawa ba za su sake haduwa da 'ya'yansu. Iyayen daliban da aka sace dai, sun shiga damuwa tare da fatan samun nasarar ceto su daga hannun 'yan binidgar. Sau da dama dai 'yan bindigar kasan sace mutane tare da yin garkuwa da su domin neman kudin fansa. Iyaye da al'ummar wannan yanki dai, sun yi fatan za a tabbatar da tsaro na din-din-din kasancewar ba yau aka soma ba.