1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kalubalen 'yancin kananan hukumomi

January 2, 2025

Kasa da 'yan makonni da tabbatar da sabon 'yancin kananan hukumomin Najeriya, ana ganin hadarin rikici tsakanin gwamnatin tarayya da ke ta kokarin lallashi da jihohin kasar da ke karatun kurma.

https://p.dw.com/p/4olYs
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Hoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

Shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu ya shaidawa wani taron gwamnonin da ke ziyartarsa a Lagos cewar, gwamnatinsa ba ta da niyyar musgunawa ko kuma kara tauye jihohin da suka dauki lokaci suna amfana daga kudi rabon kananan hukumominsu. Ya zuwa karshen watan Janairun nan ne dai, kananan hukumomin Najeriya 774 suke shirin komawa kan tsarin samun kudin shiga na kai tsaye daga tarayya. 'Yancin dai na nufin kwashe kusan kaso 45 cikin 100 na kudein da jihohin kasar ke samu yanzu haka, ko bayan rage tasirin gwamnonin cikin batun siyasa da kila ma ikonsu.

Karin Bayani: Makomar cin gashin kan kananan hukumomi a Najeriya

Aliyu Haruna Kankara dai na zaman ma'ajin kungiyar ma'aikatan kananan hukumomin kasar NULGE, kuma ya ce sabon tsarin zai inganta rayuwa da makomar miliyoyin 'yan kasar da ke ta korafi a halin yanzu. To sai dai kuma in har ana shirin jin dadi a karkara, ana kuma kallon sonsomin rikici a tsakanin gwamnonin da ke jihohin kasar da ita kanta gwamnatin tarayyar da ke daure gindin sabon 'yancin. Duk da cewar dai gwamnonin sun yi nasarar tabbatar da shugabannin kananan hukumomin daga jam'iyyun da ke tafi da mulki a jihohin, Abujar dai ta yi gargadin daure duk wani shugaban karamar hukumar da ya mika kudin karamar hukumarsa ga gwamnan jihar.

Najeriya | Majalisar Dokoki | Majalisar Dattijai
Zauren majalisar dattijan NajeriyaHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

A yayin da jihohin ke samun kaso 26 cikin 100 na kudin kasar, kananan hukumomin na samun kaso 20 domin harkokin albashi da inganta lafiya da ma ilimin miliyoyi a karkara. Shekaru can baya dai, an rika kallon takun-saka a tsakanin gwamnonin da shugabannin kananan hukumomin da ke yi wa kansu kirari na kafi gwamna. Sakamakon tasiri na ayyukan raya kasar da shugabannin kananan hukumomin suka aiwatar cikin yankin nasu. Hamisu Anani dai shugaban karamar hukumar Wase ne da ke a Plateau kuma sakataren kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi ta kasar ALGON, kuma ya ce ba hujjar rikici cikin kasar a nan gaba.

Karin Bayani: Najeriya: Yancin cin gashin kai ga kananan hukumomi

Rikici irin na gadon-gado ko kuma kokarin gyara rayuwa, kundin tsarin mulkin kasar dai ya yi daurin gwarmai a tsakanin jihohin da ke da tunani irin na babban yaya da kuma kananan hukumomin da ke fadin sun balaga. Farfesa Almustapha Osuji dai na zaman kwarrare a cikin kundin tsarin mulki, kuma ya ce da kamar wuya a ware hanta da jini. Koma wane tasiri ake shirin gani cikin sabon tsarin dai, Najeriyar na tsakanin warware rigingimun rashin tsaro da ma na talauci a cikin neman ceto ga kananan hukumomin kasar da kuma fadawa cikin wani rikicin siyasar da ke iya hargitsa rayuwa da makomar miliyoyi cikin kasar.