Sulhun Daurawa da gwamnan Kano
March 5, 2024An kawo karshen tashin-tashinar da ta kunno kai tsakanin gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif da kuma babban kwamandan Hukumar Hisbah ta jihar Malam Aminu Ibrahim Daurawa. Wasu kalaman gwamnan da ke kama da jirwaye mai kamar wanka ne dai, suka sanya kwamandan Hisbar yin fushi da tare da ajiye mukaminsa. Wannan lamari dai ya janyo zazzafar muhawara a ciki da ma wajen jihar, inda wasu ke ganin babu kuskure a kalaman gwamnan wasu kuma ke cedwa ya yi wa kwamandan gyara a bainar jama'a.
Saidai bayan shiga tsakani da Zauren Hadin kan Malaman Jihar Kano ya yi, an sasanta an kuma yafi juna. Tuni ma dai Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da ya tabbatarwa da DW cewar komai ya wuce kuma zai koma aiki ba gudu ba ja da baya, ya koma bakin aikin nasa. A ta bakin Dakta Ahmed Sa'idu Dukawa da ke zaman sakataren zauren da suka shiga tsakanin, kiraye-kirayen al'umma ne ya karfafa musu gwiwa. Shi ma da yake bayani kan batun, mukaddashin babban Hukumar ta Hisba Dakta Mujahid Aminudden Abubakar ya bayyana matukar jin dadinsa kan abin da ya ce an murkushe shaidan din da ya kunno kai a tsakani.