1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Samar da makamai da jami'an tsaron Najeriya

November 17, 2020

A yayin da ake ci gaba da fuskantar ta'azzarar rashin tsaro a sassan Najeriya, majalisar tsaron kasar ta ce tana shirin kara samar da makamai na zamani ga rundunar 'yan sanda ta kasar da nufin tunkurar matsalar.

https://p.dw.com/p/3lRZt
Nigeria Abuja | Parlament nach Schusswechsel abgeriegelt
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Kama daga babbar hanyar da ta hade Abuja da ragowar sassan arewacin Najeriya zuwa jihohin da ke arewa ta tsakiya da ma sashen kudu maso kudu dai, ana kallon ta'azzarar rashin tsaro sakamakon karuwa ta satar al'umma da ma aiyyukan 'yan kungiyoyi na asiri.

To sai dai kuma majalisar tsaron kasar ta ce tana shirin kara yawa na makamai da mai da su na zamani da nufin tunkarar matsalar da ke shirin zama ruwan dare gama duniyar kasar.  Jami'an tsaro da tallafin kudi a Zamfara.

Ko a farkon wannan mako dai an sace da dama na yan kasar a babbar hanyar da ta hade Abuja da ke zaman cibiyar mulki ta kasar da Kaduna da ke sashen arewacin kasar a wani abin da ya tada hankalin mahukuntan Najeriya.

Maigari Dingyadi dai na zaman ministan 'yan sandan Najeriya da kuma ya ce ana shirin karin azama da nufin tunkarar matsalar da ke kama da neman sa'a ta barayi maimakon rikicin da ke neman wucewa da sanin 'yan mulki na kasar.  Najeriya: Bukatar dakatar da tashin hankali  .

Nigeria Angriff von Nomaden im Bundesstaat Plateau | Sicherheitskräfte
Hoto: Reuters/Reuters TV

To sai dai koma ina makaman zamanin ke iya kai wa da nufin iya warware matsalar da ke tashi da lafawa a ko'ina cikin kasar, dai daga duk alamu da sauran tafiya a tsakanin mahukuntan kasar da kai karshen matsalar a tunanin Kabir Adamu da ke zaman masanin tsaro a kasar.  Fargabar fadawa karancin cimaka biyo bayan ta'azzarar matsalolin tsaro a arewacin Najeriya

Tun bayan zanga-zangar kai karshen 'yan sandan SARS ta matasa dai Najeriya tana kallon kari na aiyukan laifin da ake ta'allakawa da juya bayan 'yan sandan a cikin aiyukan tsaron kasar.

To sai dai kuma a fadar ministan 'yan sandan har ya zuwa jami'an 'yan sandan na ci gaba a cikin aikin gado na tabbatar da samar da tsaro a tsakanin al'umma. Babban aikin dake gaban mahukuntan tarrayar najeriyar dai na zaman iya kwantar da hankulan al'umma na kasar dake kallon dada lalacewar lamuran na tsaro amma kuma gwamnatin kasar tana fadin an nisa a cikin neman hanyar kare matsalar.