Najeriya: Karin kudi ga daliban jami'a
February 3, 2022Daukacin jami'o'i da manyan makarantun Najeriyar ne dai suka yi karin kudin, inda wasu makarantun suka kara abin da ya kai sama da kaso 100. Matakin karin kudin makarantun ya tunzura dalibai, inda suka bayyana cewa suna shirin gudanar da zanga-zanga a kasar domin nuna rashin yardarsu. Daliban jami'o'in dai sun nuna takaicinsu kan karin kudin da suka ce ya zo a lokacin da su da iyayensu ke cikin mawuyacin hali, sakamakon matsalolin koma bayan tattalin arziki. Majalisar dattawan Najeriyar dai ta shiga lamarin, a kokarin kaucewa shiga zanga-zangar da dalibana suka tsara domin nuna kin amincewarsu. Wakilan daliban dai, sun gana da shugabannin majalisar dattawan Najeriyar a Abuja.
Duk da cika alkwari da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi na karin kaso 50 cikin 100 na abin da ya kebewa ilimi a kasafin 2022, har yanzu Najeriyar ba ta kai adadin kaso 15 zuwa 20 da Hukumar Kula da Ilimi ta Majalisar Dinkin Duniya ta nemi kasashe su kebe ba. Ana dai wannan tirka-tirka ne, a daidai lokacin da gwamnatin Najeriyar ta gaza cikawa malaman jami'o'in alkawarin da ta yi musu na kudin gudanar da jami'o'in da ma alawus-alawus dinsu. Harkar ilimin boko a Najeriya dai ta dade tana cikin mawuyacin hali na rashin isassun kayan aiki da kudin gudanarwa, a daidai lokacin da ake kirkiro karin makarantun da wasu ke zama tamkar kango.