1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Togo za ta sasanta Nijar da kungiyar Ecowas

Salissou Boukari
November 7, 2023

Togo ta amince ta shiga tsakanin Nijar da sauran kasashen duniya don samun masalaha a takunkumin da ECOWAS da UEMOA suka kakaba wa Nijar bayan juyin mulki

https://p.dw.com/p/4YWxs
Ministan harkokin wajen Togos Robert Dussey
Hoto: Reuters/E. Munoz

A wata ziyara da Ministan tsaron Jamhuriyar Nijar ya kai birnin birnin Lome na kasar Togo domin neman kasar ta amince ta shige gaba kan batun janye sojojin Faransa daga Nijar, inda za su bi lamarin sau da kafa tare da Amurka. Ministan tsaron Nijar janar Salifou Mody ya ce babban abin da suke bukata shi ne Sojojin Faransa sun fice salin alin daga kasar Nijar,

Tuni dai kasar Togo ta bakin ministan harkokin wajenta Robert Dussey, ta nuna farin ciki game da amincewar da Nijar ta yi mata kan wannan batu. Kasar Togo ta ce ta amince za ta shiga tsakani domin samu mafita kan kangin da Nijar din ta shiga. 

Ministan harkokin wajen Togo Robert Dussey yace ko da yake kasarsa na adawa da juyin mulki, amma ta na goyon bayan duk wata hanya ta samar da zaman lafiya musamman ganin yadda yankin Sahel ke fama da matsalolin tsaro.

Da yake magana kan wannan batu Omar Souley, shugaban kungiyar FCR mai fafutukar kare hakkin jama'a da ci gaban dimukuradiyya ya ce fatansu shiga tsakanin ya kasance na gaskiya.

Sai dai a nasa bangaren Sahanine Mahamadou wani na hannun daman hambararren shugaban kasar Bazoum Mohamed ya ce sojoji su suka jefa kasar cikin halin da ta shiga.

Abin jira a gani dai shi ne tasirin da shiga tsakanin zai yi wajen warware matsalar Nijar da kuma sa ido don ganin sojojin Faransa sun fice daga Nijar.