1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bazoum na neman arcewa, in ji sojojin Nijar

October 20, 2023

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta sanar da cewa shugaba Bazoum ya yi kokarin kubucewa don tserewa zuwa Najeriya. Amma suka ce sun dakile yunkurin tare da gudanar da bincike a kan wannan batu.

https://p.dw.com/p/4XmYz
Shugaba Bazoum na tsare tun bayan da sojoji suka hambarar da gwamnnatinsa
Shugaba Bazoum na tsare tun bayan da sojoji suka hambarar da gwamnnatinsaHoto: Stevens Tomas/ABACA/IMAGO

Mai magana da yawun gwamnatin mulkin sojin Kanal Amadou Abdramane ne ya sanar da hakan da tsakar dare, yana mai cewa shugaba Bazoum ya yi kokarin kubucewa tare da iyalansa da kuma wasu na jikinsa da karfe uku na tsakar dare, amma tuni aka kama su tare da fara bincike a kai. Amadou Abdramane ya ce an shirya kai Bazoum  wata maboya a birnin Yamai, sannan a dauke shi da wani jirgi mai saukar Ungulu zuwa Najeriya.

Karin bayani:Matsalolin tsaro bayan juyin mulki a Nijar 

Tun a ranar 26 ga watan Yulin jiya ne sojojin suka hambarar da gwamnatinMohamed  Bazoum  sannan suka tsare shi a gidansa da ke fadar shugaban kasa tare da iyalansa, bayan da ya ki amince wa da yin murabus.