1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukukuwan Sallah a Saudiyya da sauran kasashen Musulmi

Abdourahamane Hassane MNA
April 10, 2024

Tun farko kasar Saudiyya, kasa mafi tsarkin addinin Musulunci, ta sanar cewa, a ranar Laraba ne za a fara bukukuwan Sallah na karshen azumin watan Ramadan.

https://p.dw.com/p/4ebC1
Hoto: Abdel Ghani Bashir/AFP

 Musulmi a fadin duniya na bukukuwan karamar Sallama ko kuma Eid El Fitr a wannan Laraba, bayan kammala ibadar wata mai falala na azumin Ramada. Tun a ranar Talata dai wasu kasashen ciki har da Jamhuriyar Nijar da makwabciyarta Mali suka gudanar da tasu Sallar bayan da suka ce an ga jinjirin watan Shawwal a wasu sansan kasashen. To amma a kasashen irin su Najeriya da Ghana da Saudiyya da Jamus da kuma karin wasu kasashen da dama na duniya ba a samun ganin jinjirin watan ba, lamarin da ya sa hukumomi suka bayar da umurnin a cike azumin kwanaki 30 domin gudanar da bukuwan a wannan Laraba.

Tuni ma dai a nan Jamus aka hau idi a wannan safiya ta Laraba a masallatai daban-daban na fadin kasar, yayin da a Najeriya aka gudanar bukukuwan Sallar a cikin yanayi na karfafa matakan tsaro. Jama'a ko-ina cikin kasar na ci gaba da taya juna murnar Sallah ta hanyar ziyarce-ziyarce da kuma nishadi.