Kasashen duniya na fuskantar barazanar ballewa
October 5, 2017Talla
Kasar kamaru na daga cikin kasashen Afirka da a yanzu suka shiga jerin kasashen da ke cikin rikicin neman ballewa da yankin masu magan da Turanci ke ikirari, ko da ya ke Najeriya da ke makotaka da Kamaru suna kokarin shawo kan rikicin 'yan yankin Igo da ke fafitikar kafa kasar Biafara a Kudu maso Kudancin kasar.
Su kuwa Kurdawa a kasar Iraki, sun gudanar da zaben raba gardama na neman raba gari da gwamnatin Bagadaza, inda tuni suka fitar da jadawalin zabubbukan yankin, ko da ya ke suna fuskantar wariya daga kasashe makota.
Kasar Spaniya ma dai ana ta rikita-rikita bayan da 'yan yankin Kataloniya suka jefa kuri'ar neman ficewa daga kasar, sai dai kotun birnin Bercelona sun haramta zaben a tun farko.