1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Binciken ayyukan 'yan bindiga a Katsina

May 24, 2023

Majalisar Dinkin Duniya, ta bude cibiyar bincike kan ayyukan 'yan bindiga a jihar Katsina da ke Tarayyar Najeriya.

https://p.dw.com/p/4RmEh
Najeriya | Tsaro | Katsina
Ko da a kwanakin baya ma, sai da matasa suka jagoranci zanga-zanga kan rashin tsaroHoto: DW/H. Y. Jibiya

Majalisar Dinkin Duniyar ta bude cibiyar ne, domin yin nazari kan matsalar tsaro da hanyoyin da za abi wajan magance ta da kuma bincike kan abin da yasa 'yan bindigar suka dau makamai suna kashe al'umma. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da take gudanar da binciken a jihohin Arewa maso Yammacin Najeriyar da ke fama da hare-haren 'yan bindiga, inda ta samu bayanai daga mahukuntan jihar da suka karfafa mata gwiwar bude cibiyar domin bayar da gudummawa wajen shawo kan matsalar tsaron. Ibrahim Ahmed Katsina shi ne mai bai wa gwamnan jihar ta Katsina shawara kan harkar tsaro, ya ce sun samu gudummawa sosai daga Majalisar Dinkin Duniya wajen inganta cibiyar.

Najeriya | Matsalar Tsaro | Arewa maso Yamma | Zanen Barkwanci
Jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya, na fama da tarin matsalolin tsaro

Mai bai wa gwamnan shawara kan tsaron ya ce cibiyar na da matukar amfani, wajen magance dalilin faruwar matsalar tsaro a jihar da kuma lalubo hanyoyin da suka sa aka samu matsalar. Acewar masana tsaro kamar Malam Bala Abdullahi bude cibiyar abu ne mai kyau musamman yadda yanzu komai ya koma na zamani, hakan zai taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan matsalar. Sai dai masana harkar sadarwa a Najeriyar na ganin lallai sai wadanda aka dorawa alhakin tafiyar da cibiyar sun sa kishin kasa, za a iya samun nasarar da ake nema. Tuni dai aikin wannan cibiya ya fara kankama, kuma kawo yanzu rahotanni sun nuna al'umma a jihar Katsina sun fara samun saukin matsalar tsaro musamman idan aka yi la'akari a baya a rana daya 'yan bindigar kan kai harin da za su halaka mutane fiye da 50.