1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Kayan agaji sun sake isa Zirin Gaza

October 22, 2023

A wannan Lahadin, motoci 17 na kayan agaji ciki har da wadanda ke dauke da man fetur ne suka sake shiga Zirin Gaza a karo na biyu ta mashigin Rafa.

https://p.dw.com/p/4XsIC
Motocin kayan agaji a iyakar Rafah
Motocin kayan agaji a iyakar RafahHoto: Ibraheem Abu Mustafa/REUTERS

Wannan dai shi ne karon farko da aka shigar da man fetur zuwa Gaza tun bayan fara rikici tsakanin Isra'ila da Hamas. Ana sa ran motoci shida da ke dauke da man fetur su isa zuwa asibitoci guda biyu na Gaza.

Motocin dai sun taho ne daga kasar Masar, inda jami'ai suka gudanar da bincike kafin ba su izinin shiga Zirin Gaza.

Karin bayani:Rukunin farko na motocin kayan agaji ya isa Gaza 

Tun a jiya Asabar ce Majalisar Dinkin Duniya ta nuna farin cikinta na shigar da rukunin farko na kayan agaji zuwa Gaza, sai dai kuma ta ce kamata ya yi a kalla motoci 100 su shigar da kayan agaji zuwa Gaza a kowace rana.

A cewar MDD, da kamar wuya a iya samun abinci ko ruwa a yankin tun bayan da Isra'ila ta dakatar da shigar kaya yankin sakamakon rikicin.