Masar na taron zaman lafiya kan rikicin Gaza
October 21, 2023A makon da ya gabata ne dai kasar Masar ta kira taron domin shawo kan rikici da kuma sanin makomar Falasdinawa.
Ministan harkokin wajen Masar, Sameh Shoukry ya ce taron zai mayar da hankali ne wajen ganin an tsagaita bude wuta da kuma kai kayayyakin agaji zuwa zirin Gaza.
Karin bayani: Chaina za ta hada hannu da Rasha don magance rikicin Gaza
Kasar Masar da ta shirya taron, kana kasar Larabawa ta farko da ta sanya hannun kan yarjejeniyar zaman lafiya da Isra'ila a shekarar 1979 ta damu matuka kan yadda jama'a a zirin Gaza za su kaura zuwa yankinta.
Karin bayani: Masar: Adawa da kwararar 'yan gudun hijira
Kafafen yada labaran kasar Masar sun ruwaito cewa daga cikin wadanda za su halarci taron har da shugaban Faladinawa Mahmoud Abbas da takwarorinsa na Jordan da kuma Italiya da ma babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres.