Kayan karatun yara masu lalurar ido sun yi karanci a Afirka
January 4, 2024A wani sabon binciken da kungiyar kare hakkin masu bukata ta musanman a Afrika mai suna "Beyound the border of disabilty" ta gudanar, ta bayyana karara cewar tsadar na'urar da ke tallafa wa katatun 'masu larurar ido (Braille machine) na dakushe masu gwiwa wajen neman ilmi. Rilwanu Abdullahi, shugaban wannan kungiya ya bayyana cewar akwai matsoli da dama da ke shafar ilmin yara da ke da matsalar idanu a kasashen Afrika, inda talauci ya kasance daga cikin manyan kalubalen da ke haddasa iyaye gazawa wajen biya wa 'ya'yansu kudaden karatu da kayayyakin karatu.
Karin bayani: Tunawa da ranar mutane masu bukata ta musamman
Rilwanu ya ce tsadar kayayyakin karatun yaran da ke da lalurar gani ya fi kowane bangaren ilimin yara a kasashen.Afrika sakamakon yadda rayuwa ta sanya wasu iyaye barin 'ya'yansu akan titi da kokon bara. Ya ci gaba da cewar, ana sayar da Na'urar karatu a kan Naira 250 000. Saboda haka ne suke yin kira da babbar murya ga masu ruwa da tsaki a kan tallafa wa wadannan yara don ceto rayuwarsu daga duhun jahilci.
Karin bayani: Neman mafita kan tabarbacewar ilimin yara
Sauran kayayyakin karatun sun hada da allon karatu da alkalami, wanda su ma farashin ya yi tashin gwauron zabi a kasuwannin Najeriya. Wannan na zuwa ne daidai lokacin da duniya ke bikin 04 ga watan Janairu a matsayin ranar tunawa da na'urar da ke taimakawa masu larurar gani wajen karatu da sauran hanyoyin neman ilmin zamani.