Magance matsalar rashin ilimi a Yobe
July 2, 2019Shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya na cikin yankunan da aka fi samun yara da ba sa zuwa makaranta, inda alkaluma ke karuwa saboda matsalar kungiyar Boko Haram da ke yaki da karatun Boko, abin da ya haifar da matsalar tsaro da ta kara dagula harkokin ilimin. A cewar masana akwai miliyoyin yara da ke tsakanin shekaru shida zuwa 14 da ba sa zuwa makaranta a Najeria, daga cikin alkaluman kaso 69 cikin 100 daga yankin arewacin Najeriya su ka fito.
Domin magance wannan matsala ne ma gwamnatin jihar Yobe da ke yankin na Arewa maso Gabashin Najeriya da rashin tsaron ya fi kamari, ta tara masana a dukkanin fannoni domin lalubo mafita ta magane matsalolin ilimi, ba kawai a jihar ba har ma da shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriyar.
Shehunan mamalai na manyan jami'o'i da sauran masu ruwa da tsaki sun kwashe tsawon kwanani biyu su na tattaunawa, inda a karshe su ka fito da shawarwari da ya kamata gwamnatoci su dauka domin magance matsalar a jihar ta Yobe. Daga cikin shawarwarin da su ka bayar akwai batun gyaran makarantun da kyautata rayuwar malamai gami da ci gaba da horar da malamai da kuma tabbatar da iyaye a nasu bangaren na tura 'ya'yansu makaranta. Haka kuma taron ya bayar da shawarar bai wa sarakuna damar sa ido kan yadda al'ummar su ke tura yaransu daga maza har matan zuwa makarata gami da kara yawan makarantu da inganta karatun yaki da jahilci da ilimin nakasassu da marayu da kuma habaka karatun tsangaya da ilimin kimakiyaya.
Tuni dai gwamnan jihar Yoben Mai Mala Buni ya kafa kwamitin kwararru da zai jagoranci aiwatar da shawarwarin masanan, inda ya ce burin 'ya'yan talakawa da sauran marasa karfi shi ne su shiga aji guda da 'ya'yan masu hannun da shuni domin samun ilimi ba tare da wani banbamci ba.