Kim Jong Un na ci gaba da ziyara a Rasha
September 16, 2023Dama a lokacin da ya gana da takwaransa Vladimir Putin shugaban ya sanar da cewa Kim Jong Un zai halarci wani kasaitaccen atisayen jiragen ruwan yaki da za a gudanar a tekun Pacific.
Karin bayani: Shugaba Kim ya gana da Putin
Tuni dai kasashen Yamma ciki har da Amurka suka fara martani kan ziyarar, suna masu zargin Moscow da neman cefano makamai daga Piyongyang domin kara karfin sojojinta da ke daga a Ukraine, yayin da ita kuwa Koriya ta Arewa ke neman mallakar fasahohin zamani domin ingata shirinta na Nukiliya da kera makamai masu linzami.
Karin bayani: Ziyarar Kim ga Putin ta sa Amurka fargaba
A yayin ziyarar da ya fara a ranar Talata (12.09.2023) wacce ke zama ta farko tun bayan barkewar annobar Covid-19, shugaba Kim Jong Un ya gayyaci takwaransa Putin zuwa Koriya ta Arewa, sai dai ba bu wata matsaya a hukumance da shugabannin biyu suka cimma a cewar kakakin gwamnatin Rasha Dmitry Peskov.