1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tsohon shugaban Najeriya ya nemi kyautata mulki a Afirka

Uwais Abubakar Idris SB/ZUD
March 6, 2024

Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana bukatar kasashen Afirka su fito da tsarin dimukuradiyya irin na Afirka da ya dace da nahiyar, saboda samun mafita kan kalubalen da ake ciki a nahiyar.

https://p.dw.com/p/4dEpy
Cif Olusengu Obasanjo tsohon shugaban Najeriya
Cif Olusengu Obasanjo tsohon shugaban NajeriyaHoto: Minasse Wondimu Hailu/Anadolu Agency/picture alliance

Tsohon Shugaba Cif Olusegun Obasanjo na Najeriya ya bayyana bukatar kasashen Afirka su fito da tsarin dimukuradiyya irin na Afirka da ya dace da nahjiyar domin zama mafita daga kalubale na rashin ci gaba saboda yadda shugabanin ke gudanar da mulki. Amma dimukurdiyyar bata dace ba ko shugabanin da ke aiwatar da ita?

Karin Bayani: An cimma yarjejeniyar sulhu a Ethiopiya

Shugabannin Afirka
Shugabannin AfirkaHoto: MICHELE SPATARI/AFP

Nahiyar Afirka da ta rungumi tsari na dimukurdiyya dea ta aro ta yafa daga kasashen trurai, tsarin da yam aye gurbi wanda suke da shi na sarakunan gargajiya da ma kawar da sojoji daga mulki. Gazawar da ake gani ta mulkin dimukurdiyyar ko dai na shugaba mai cikakken ikon na Amurka ko kuma tsarin firaminsta na kasar Birtaniya. Wannan ya sanya tsohon shugaban Najeriya bayyana cewa akwai bukatar Afrika ta fito da tsarin dimukuradiyyar da ya dace da ita.

Sake kutse da sojoji ke yi a fagen mulki a kasashen Afirka da dama musamman ma dai a kasashen na Afirka, inda a baya baya nan sojojin suka kifara da tsarin dimukuradiya a kasdashen Mali, Burkina Faso, Jamhuriyar Nijar da ma Guinea ya sanya sake duba me ke faruwa ne. A lokacin da wannan ke faruwa a Afirka a yanzu a kasashen Turai ma kanwar ja ce, domin masana a fanin kimiyyar siyasa sun bayyana yadda tsarin dimukuradiyyar ke fsukantar sauye-sauye.

Masu goyon bayan sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
Masu goyon bayan sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar NijarHoto: Balima Boureima/AA/picture alliance

Kiran da Cif Obasanjo ya yi da ya kara amon wannan batu da aka dade ana yi na kara tabbatara da buklatar ci gaba da amfani da tsain dimukurdiyyar domin shine ya bada damar samun gwamnati ta jama'a kuma domin jama'a. Dr Aisha Laraba Abdullahi tsohuwar kwahiniyar kula da harkokin siyasa a kungiyar tarayyar Afrika ta ce babu zabi domin mulkin soja ba zai taba samar da mafita ba.

Da alamun kasashen Afirka za su ci gaba da lalubi a kokarin samar da tsarin dimukuradiyyar da zai dace da al'addu, adini da ma yanayin zamantakewar alumamrsu domin samar da mulki bisa kamanta adalci da shine zai sanya samun ci-gaba mai dorewa a nahiyar da ke fuksntara babban kalubale na koma baya, talauci da rigingimu.