COVID-19: Koma baya a yaki da jahilci
September 8, 2020Akwai daruruwan mutane da yanzu haka ba sa zuwa makaranta duk da kokarin da ake yi na samar musu da ilimi ko kuma yakar jahilci musamman a yankunan arewacin Najeriya, wanda suke a sahun baya tsakanin takwarorinsu na sauran shiyyoyin kasar. Malam Muhammad Nazir na cikin wadan suke nuna damuwa da ma fushi na yadda karatunsu yake tabarbarewa saboda dakatar da karatun da ake yi.
Karin Bayani: Matakan yaki da jahilci a Najeriya da Nijar
Ba kawai karatun manya ne ya samu koma baya ba, akwai a makarantun yara ma kamar firamare da sakandare wanda saboda rufe su aka dubban yara da aka fitar da su daga makaranta ko dai saboda yi musu aure ko kuma kai wurare koyon sana'a. Karancin yara da ke zuwa makaranta a Najeriyar dai ya haifar da gagarumar matsala, musamman kasancewarsu masu zama manyan gobe.
To sai dai a cewar Malam Abdullahi Shu'aibu har yanzu hukumomi ba su dauko hanyar yaki da jahilci ba. Duk kokarin da DW ta yi na samun bangaren hukumomi domin sanin yadda cutar ta COVID-19 ta shafi batun na yaki da jahilci bai yi nasarar ba.
Karin Bayani: Rufe makarantun tsangaya saboda corona a Najeriya
Amma a cewar Malam Abubakar Garba Hamisu matukar hukumomi suna so a cike gurbin abin da aka rasa a karatu, dole sai sun yi abin da ya kamata. Masana da masharhanta na ganin ko bayan cotar coronavirus sai an magance matsalar tsaro da tashin hankali da ke addabar jihohin arewacin Najeriya, matsalar da ake dangantawa da kungiyar Boko Haram da ke yaki da karatun zamani, matukar ana son karatu da yaki da jahilci siu cimma nasarar.