1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Komawa gida cikin fargaba a Borno

May 22, 2019

Daruruwan mutane sun shiga fargaba bayan da rundunar sojoji ta sake kwashe wasu al’ummomin Sabongari zuwa sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Damboa mai nisan kilomita 70 daga Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno.

https://p.dw.com/p/3ItjG
Nigeria | Flüchtlingslager in Pulko
Nan ma wasu 'yan gudun hijira ne gaban dakunan wucin gadi a garin Pulka jihar BornoHoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

Tun daga ranar Litinin da ta gabata ne dai rundunar sojojin Najeriya suka tara mutanen garin Sabongari da kewaye tare da sanar da su cewa za a kwashe su zuwa wasu sansanonin ‘yan gudun hijira da ba su bayyana ba.

Daga nan ne mutanen yankin cikinsu ya duri ruwa inda wasu tun a cikin daren Talata suka fara tserewa zuwa wasu yankuna saboda ba su san manufar matakin sojojin na kwashe su daga garuruwansu ba, ga kuma da yawansu ba sa son zaman sansanonin ‘yan gudun hijira.

Malam Haruna Sabongari wani ne da ya bi jeji tare da abokansa inda suka yi dace suka samu kansu a Maiduguri, ya ce mutanen da aka kai sansanin an ajiye su ba abinci sun kai azumi ruwa kawai aka ba su.

Nigeria | Flüchtlingslager in Pulko
Rayuwar hijira cike take da kalubaleHoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

Yanzu haka daruruwan mutane da aka kwaso daga Sabongari na zube a sansanonin ‘yan gudun hijira ba tare da wurin zama ko kuma abin da za su ci ba.

Wani matashi da ya ce sunansa Isa wanda shi ma ya zabi gudowa Maiduguri maimakon jira akai shi sansanin ‘yan gudun hijira ya ce gudun sake fadawa wahala ya sa suka gudu.

Al’ummar yankin dai sun fara yin kiraye-kirayen ga shugaban kasa da ya cire manyan hafsoshin tsaro matukar ana son magance matsalar tsaro da ta addabi yankin kamar yadda Malam Abubakar Adamu ya bayyana.

Ko a kwanakin baya ma dai sojojin sun kwashe wasu al'ummomi a Jakana da ke kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri inda daga baya aka mayar da su bisa dalilai da sojojin  suka bayyana da cewa suna aikin kakkabe mayakan Boko Haram a yankunan ne.