1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministocin da ke takara a Najeriya tilas su yi murabus

Ubale Musa SB)(LMJ
May 11, 2022

Bayan dogon lokaci ana takun saka, Shugaba Muhammad Buhari na Najeriya ya umarci daukaci na ministocin gwamnatinsa da ke sha'awa ta takara da su ajiye mukaminsu, haka wani hukuncin kotu ya tabbatar da umurnin.

https://p.dw.com/p/4B9Bw
Saka hannu kan dokar zaben Najeriya
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan gami da ta wakilai Femi GbajabiamilaHoto: Nigeria Prasidential Villa

Daukacin rikicin cikin gidan jam'iyyar APC dai ya yi aure ne ya kuma tare a gindin jami'ai na gwamnatin tarrayar da ke sha'awar taka rawa a cikin fagen siyasa ta kasar. Duk da cewar dai buri ya yi nisa kama daga masu neman gadar shugaban kasar ya zuwa ga masu bukatu na kanana na mukamai dai, daukacin ministoci na gwamnatin dai sun yi watsi bisa umarnin dokar zaben kasar da ta nemi su ajiye aiki akalla wwata guda kafin zaben share fage.

Akalla ministoci guda biyar ne dai suka cika form din neman gadon Shugaba Muhammadu Buharin ko bayan wasu guda biyu da ke neman gwamnoni a jihohinsu. Kuma duk sun raba kafa tsakanin aikin ofis da kuma zagaye zuwa sassa na kasar a cikin neman cika burin mai tasiri.

Karin Bayani: Jam'iyyar APC ta kammala cinikin fom

To sai dai kuma shugaban kasar ya ce ta kare tare da wani umarnin saukar daukacin masu takarar kafin ranar Litinin ta makon gobe.

Afirka Najeriya jam'iyyar APC, Abuja
Abdulllahi Adamu Shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya da jiga-jigan jam'iyyarHoto: Ubale Musa/DW

A ranar Laraba ta makon gobe ne dai jam'iyyar ta tsara zabe na fidda gwani na zaben gwamnan APC, kafin kuma ta yi babban taro na zaben dan takara ta shugaban kasar a 30 ga watan mayun da muke ciki. Abin da ke nufin kasa da kwanaki 30 da dokar zaben ta tanada ga masu bukata ta takara da kuma ke iya sake jefa masu tsintsiyar cikin babban rikici.

Rikicin dai ya kai jam'iyyar zuwa ga asarar zaben gwamna a Zamfara, rikicin kuma da APC ke neman kaucewa yanzu. Da ranar yau dai dama kotun daukaka kara da ke Abuja dai ta sa kafa ta shure tunanin ba da hujjar ke dogaro da kai wajen ci gaba bisa mukaminsu.

Sabon hukuncin dai na iya sauya da dama cikin fagen siyasa ta kasar in da kai ke rabe a tsakanin jami'an da ke fadin ba hujja da kuma ragowwa na masu takara na wajen da ke tunanin yiwuwar amfani da mukamai wajen neman cika burin son rai.