1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamhuriyar Kwango

Kotu ta tabbatar da wanda ya lashe zabe a Kwango

January 10, 2024

Kotun tsarin mulki a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, ta tabbatar da Shugaba Felix Tshisekedi a matsayin wanda ya lashe zaben kasar da aka kammala a baya-bayan nan.

https://p.dw.com/p/4b4e6
Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: AFP

A cewar kotun Shugaba Felix Tshisekedi wanda zai fara wa'adi na biyu, ya samu kashi 73.47 cikin 100 a zaben, abin kuma da ya ba shi galaba gagaruma.

A ranar 20 ga watan jiya na Disamba ne dai aka yi zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar kasa da na shiyoyi, zaben da 'yan hamayya suka bayyana shi da wani dodo-rido.

Su dai 'yan hamayyar da suka bijire, sun bukaci da a sake zaben ne bayan kira ga magoya bayansu da su kaurace wa tsarin baki daya.

Wanda ya zo na biyu a zaben a cewar kotun na Kwango dai, shi ne Moise Katumbi, wanda ya samu kashi 18%.

Martin Fayulu ya tashi da kashi 4.9 sannan kotun ta ce mutumin nan da lashe kyautar Nobel Dr. Denis Mukwege, bai ma samu ko da kashi daya cikin 100 ba.