Najeriya: Sabuwar barazana ga 'yan soshiyal media
August 27, 2024Mai shari'a ta kotu Fati Hassan ita ce ta aike da matashi Shafi'u Umar Tureta gidan kurkuku, bayan da aka samu matashin da laifin wallafa wasu bidiyoyi a kafar intanet, guda na matar gwamana tana watsa dala, kuma tun bayan aikewa da matashin kungiyoyin kare hakkin bani Adama irinsu Amanesty International da kungiyoyin matasa suka suna ta bayyana bakin ciki da rashin jin dadi dangane da matakin gwamnatin Jihar Sakoto na saka takunkumi ga fadin albarkacin baki.
Ibrahim Adamu Tudun Doki shi ne shugaban gamayyar kungiyoyin kare hakkin dan Adam a Jihar Sakkwato.‘'A demokradiyya mutane suna da dama suna da hakki na su yi wannan korafi, ko kuma su yada don saboda a yi hir a kan Allah waddai na yadda ake irin wannan barnar da dukiyar al'umma.''
Suma dai gamayyar kungiyoyin matasa a Jihar Sakoton sun kira wani taron manema labarai inda suka bayyana matsayarsu dangane da tsare wannan matashi Shafi'u Umar Mansur Muhammad Sani shi ne ke magana da yawun wadannan matasa. ‘'Abun da aka yi ne ya sa mu mayar da martani, ba mu ga wata doka da ta hana mu yin haka nan.Gwamnati muke so ta duba da kuma hukumar jami'an farin kaya DSS su da ke da alhakin duba ya rataya ga kan su, su yi ma wannan yaron adalci.''