1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kuskure aka samu a hukuncin zaben gwamnan Kano -Kotu

Ubale Musa Abdoulaye Mamane (LMJ)
November 23, 2023

A yayin da ake cigaba da tafka muhawara kan hukuncin shari'ar gwamnan Kano, kotun daukaka kara ta ce tana shirin yin gyara bisa kuskuren alkalimi na hukuncin da ta yanke

https://p.dw.com/p/4ZMDl
Najeriya I Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf I Dr. Nasiru Yusuf Gawuna
Najeriya I Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf I Dr. Nasiru Yusuf GawunaHoto: Private/Bashir Ahmad/Facebook

Wata sanarwar kotun ta ce hukuncin da ta yanke  tun a ranar Juma'ar makon jiya a na zaman daram, kuma kuskuren dake cikin takardun shari'ar tuntuben alkalami ne da take shirin ta gyara da zarar bangarorin biyu sun nemi haka. An dauki dogon lokaci ana al'ajabi bisa banbancin da ke tsakanin matsayin kotun da kuma hukuncin da ke a takardar cikin gidan alkalan.

Kafin sabon matsayin da a cikinsa kotun tace hukuncin na Juma'a bai sauya ba, kuma tana da ikon gyara bisa ko ma mene ne yake cikin takardar, matakin kuma da daga dukkan alamu ke neman kara kawo rudani maimakon gyara a tunani.

Karin Bayani:  Jam'iyyar NNPP ta ce s kotun Abuja ta bai wa nasara a Kano

Gyara irin na gangar Auzin ko kuma neman ingantar lamura na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya isa kotun koli,tare da neman watsi da wani bangare na hukuncin da ya tsige shi kan mukamin da kuma neman kotun ta tabbatar da bangaren da ya bar masa ikon mulkin jihar Kano.

Najeriya I Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Najeriya I Gwamnan Kano, Abba Kabir YusufHoto: Kyusufabba/Twitter

Koma ya take shirin kayawa a gaban kotun kolin, ga dukkan alamu shari'ar jihar Kanon na shirin zama wani zakaran gwajin dafi bisa makomar shari'un zabe na kasar Najeriya.

Karin Bayani:  Kotu ta yanke hukuncin zaben gwamnan Kano

Daukaci na masu adawa na kallon abun dake faruwa cikin zauren alkalan na iya komawa barazana bisa ga tsarin demokaradiyya ta kasar, inda masu sharhi kan harkokin cikin gida a Najeriya kamar su Auwal Rafsanjani, na kungiyar Transparency mai yakin hanci ke cewa "Alkalan suna bukatar wankan tsarki da nuifn ceton suna da kila ma kimar su." Gyara cikin gidan alakaln na da tasirin gaske a kokarin girka demokaradiyyar Najeriya.