1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kano: Dakon ranar yanke hukuncin karshe

December 21, 2023

Bayan tsawon lokaci ana jiran kotun kolin Najeriya ta bude sauraron karar zaben gwamnnan jihar Kano, daruruwan magoya bayan jam'iyyar NNPP mai mulki a Kanon da ma APC ta adawa sun yi tururuwa zuwa harabar kotun.

https://p.dw.com/p/4aRKi
Najeriya | Kano | Zabe | Shari'a | Kotun Koli | Abba Kabir Yusuf  | Nasiru Yusuf Gawuna
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ad abokin hamayyarsa Nasiru Yusuf GawunaHoto: Private/Bashir Ahmad/Facebook

Shari'ar da ke matakin karshe dai na zaman mafi daukar hankali a daukacin zaben gwamnonin  Najeriyar a halin yanzu. Bayan alkalan kotun kolin sun kwashe tsawon sa'o'i sama da uku suna sauraron shari'ar, lauyoyin bangarorin biyu sun kare muhawara da ma bayar da hujjojjin da suke fatan ka iya burge alkalan kotun ta Abuja. Duk da cewar dai an dage zaman ba tare da saka ranar yanke hukuncin da ke da tasiri ba, dokar zabe da kila ma kundin tsarin mulkin kasar sun tanadi yanke hukunci kan batun kafin ranar 14 ga watan Janairun gobe. To sai dai kuma an kare tare da babban fata a bangarorin da ke ta kokawar neman sa'ar kotun, kamar yadda Hashim Suleman da ke zaman shugaban jam'iyyar NNPP a Kanon ke bayyana kwarin gwiwa.

Najeriya | Abuja | Kotun Koli | Sauraro | Shari'a | Gwamna | Kano
Harabar kotun kolin Tarayyar NajeriyaHoto: U.A. Idris

Koma menene ya bai wa masu kayan dadin kwarin gwiwa ga suma masu takama da tsintsiyar share dattin dai, hujjojjin da suka gabatar a gaban kotun sun isa kai su ga bacci a kwanciya ta hankali a fadar Abdullahi Abbas da ke zaman shugaban jam'iyar APC a Kanon. Rudani cikin gidan alkalai, ko kuma son ran da ke tayar da hankali ko bayan fuskar fatan da ke ta annuri a waje, can a zuciya dai akwai alamun komawa ga mai duka a bangaren masu siyasar da ke da damar karshe cikin gwagwarmaya ta mallakar Kanon mai tasiri. Mulkin cikin Kano har Mahadi ko kuma kokarin jefa jihar cikin rudani, akwai dai tsoron barkewar rikici a Kanon da ke zaman ruhi na siyasa ta kasar. Salihu Sagir Takai dai na zaman jigon jam'iyyar APC a Kano, kuma a cewarsa ba zabi face zaman lafiya cikin jihar ko ma mai zai faru. Abun jira a gani dai na zaman saka ranar yanke hukunci a bangaren alkalan da ke da jan aikin yanke hukuncin wanda ko bayan batun na hujjar doka, ka iya kwantar da hankalin miliyoyi 'yan kasar da ke kallon shari'ar da idanu na gazawa.