1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta musanta sayen makaman Koriya ta Arewa

September 15, 2023

Shugaba Putin ya ce ko da ya kulla alakar soji da Koriya ta Arewa, hakan bai kamata ya sanya duniya damuwa ba, domin shi bai ga wani abun tayar da jijyoyin wuya ba.

https://p.dw.com/p/4WOxA
Hoto: Sputnik/Mikhail Metzel/Kremlin via REUTERS

Fadar Kremlin ta gwamnatin Rasha ta sanar da cewa babu wata yarjejeniya da Shugaba Vladimir Putin ya kulla da shugaban Koriya ta Arewa. Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Kasashen Yamma ke fargabar wadannan kasashe biyu da suke tsama da su sun kulla yarjejeniyar musayar makamai masu hatsari a tsakaninsu.

Shugaban na Rasha ya musanta zargin da wasu kasashen Yamma ke yi na cewa yana saba ka'idar haramta sayen makamai daga Koriya ta Arewa da MDD ta ayyana.

Tun a ranar Laraba ce dai Shugaba Kim na Koriya ya isa kasar Rasha, a wata ziyara da ke ci gaba da daukar hankalin manyan kasashen duniya. A wannan Juma'ar kuma an ruwaito cewa Shugaba Kim Jong Un ya duba wani jirgin yaki a gabashin Rasha.