Najeriya: Kwalara ta haddasa asarar rayuka
July 29, 2021Masana da masu yaki da cutar kwalara har da al’umma sun nuna damuwa kan yadda wannan cuta take yaduwa kamar wutar daji da yanzu alkaluma suka nuna cewar mutane dubu 19,305 daga farkon shekarar nan zuwa yanzu suka kamu. Wata matar da ke ammsa tambayoyin likita a daya daga cikin wuraren da aka ware domin kula da wadanda su kamu da cutar amai da gudawa da ake kira da sanun kwalara ta ce sun wahala sossai a sakamakon cutar. Alkaluman da hukumar kula da yaduwar cututtuka ta Najeriya ta fitar na yawan mace-mace da aka samu daga barkewar cutar amai da gudawa sun tada hankulan al’umma da masana saboda yadda take yaduwa kamar wutar daji ta na hallaka mutane. A cewar hukumar kusan mutane dubu 20 suka mu da cutar a Jihohin Gombe da Yobe da birnin tarayya Abuja gami da wasu jihohin 16 na kasar inda mutane kusan dari biyar suka mutu sandiyyar wannan cuta.
Sakacin jama'a na daga cikin dalilan da kan janyo yaduwar cutar kwalara a arewacin Najeriya
Kungiyoyin da sauran daidaiku da ke yaki da yaduwar wannan cuta sun bayyana cewa akwai sakaci na jama’a wanda shi ne ke bude kofa ga yaduwar cutar a kusan dukkanin sassan kasar. Su ma al’umma sun amince da cewa yanayi da suke da ma wuraren da suke zama na kunshe da hanyoyin yaduwar wanann cuta kamar yadda Kolomi Mustapha ya bayyana. Kokarin ji daga bangaren hukumomin Najeriyar ya ci tura don kuwa wakilin DW Hausa ya nemi lambobin jami’an hukumar lafiya don sanin matakai da suke dauka sai dai wayoyin nasu ba su shiga.