Lauyoyin Kenya na kokarin hana a kai 'yan sanda Haiti
May 18, 2024Talla
Wannan yunkurin na lauyoyin na zuwa ne kwanaki gabanin jami'an 'yan sandan su isa kasar domin kwantar da tarzoma.
Babbar kotun kasar ta bayar da umurnin cewa a mika bukatar ga manyan jami'an gwamnatin kasar kana ta daga saurar karar zuwa ranar 12 ga watan Juni na shekarar 2024.
Karin bayani: 'Yan Kenya na adawa da matakin gwamnatin na tura 'yan sanda a Haiti
Tun dai a watan Yulin bara ce, kasar Kenyar ta yi tayin tura wa Haiti jami'ai 1,000 domin taimaka wa kasar wajen magance matsalar tabarbarewar tsaron da ta ke fuskanta. Kasashen Jamaica da Bahamas da Benin da Chadi da kuma Bangladesh suma sun yi alkawarin tura wa Haitin jami'an kwantar da tarzoma.