1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKenya

Kenya: Muhawara a kan tura 'yan sandan kasar zuwa Haiti

Edith Kimani AMA
April 2, 2024

Shugaban Kenya William Ruto ya shiga halin tsaka mai wuya bayan da gwamnatinsa ta amince ta tura 'yan sandanta zuwa Haiti,

https://p.dw.com/p/4eLsT
Hoto: Richard Pierrin/AFP/Getty Images

 Haiti dai ta fada cikin tashin hankali tun wtanni biyu da suka gabata, kuma ta jima ba tare da tabbataccen shugaban kasa ba, tun bayan kisan gillar da aka yi wa tsohon shugaban kasar Jovenel Moise a shekarar 2021. Yanzu haka dai kaso mafi yawa na Port-au-Prince babban birnin kasar na hannun gungu biyu na 'yan tarzomar da basa ga maciji da juna, wadanda suka kona wurare da dama na cibiyoyin gwamnati. Elidor Samuel wani bakanike ne da 'yan dabar suka kona wa rumfar gyaran motoci, ya ce yanzu rayuwa ta shiga kangi marar misaltuwa: "Wannan kasa yanzu sam ba wurin zama ba ne ga 'dan Adam, domin matasanmu da ke da sana'o'in yi ba su da damar iya yin komai, kasancewar komai na ci gaban rayuwa ya tabarbare, an kona komai da mutum zai mora".

Har yanzu ana cikin mawuyacin hali a Haiti

Proteste in Haiti
Hoto: Odelyn Joseph/AP/picture alliance

To sai dai duk da halin da kasar take ciki, shugaban Kenya William Ruto ya ce akwai mafita da yake ganin za ta haifar da wanzuwar zaman lafiya mai dorewa a kasar. Dama dai a cikin watan Maris da ya gabata ne ya amince da aikewa da 'yan sandan kasarsa 1000 zuwa Haitin, domin aikin wanzar da zaman lafiya na hadin gwiwa, don agazawa jami'an tsaron kasar: "Babban abin da ke da muhimmanci da ake bukatar hanzarta samarwa shi ne tabbatar da jin kai da kare hakkokin al'ummar Haiti,  maza da mata".

William Ruto ya ce za a iya shawo kan matsalar Haiti

William Ruto shugaban kasar Kenya
William Ruto shugaban kasar KenyaHoto: Khalil Senosi/AP/picture alliance

Wannan yunkuri na shugaba Ruto ya fuskanci adawa mai zafi daga al'ummar Kenya, inda wasu ke ganin shirin a matsayin hanya ta yin rub da ciki da makudan kudi, sakamakon yadda Amurka ta ware Dala miliyan 100 domin tabbatar da nasarar aikin.  George Musamali, wani mai sharhi ne kan al'amuran tsaro a Kenya, ya ce kasarsu ba ta da wata rawar takawa a wannan shirin, face dai muradin cimma wata gidoga ta bayan fag: '' 'Yan sandanmu za su je ne a matsayin sojojin haya, wadanda aka bai wa makamai aka kuma biya su, wannan shi ne abin da yake faruwa ai ga sojojin haya. Don haka wannan sam ba daidai bane".

Al 'ummar Kenya na yin adawa da shirin gweamnatin na tura 'yan sandanta a Haiti

Frankreich fliegt 240 Menschen aus Haiti aus
Hoto: Orlando Barria/EPA

Kenya na da tarihin aikewa da 'yan sandanta zuwa kasashen duniya don aikin wanzar da zaman lafiya, inda a baya ta tura dakarunta zuwa Laberiya da Yugoslavia. Wadanda ke goyon bayan wannan shiri a Kenya sun ce akwai nauyin da ya rataya a kanta na agaza wa aminanta a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. To sai dai baya ga batun yaukaka alakar diflomasiyya, akwai kalubale ta fuskar shari'a, domin ko a cikin watan Janairun da ya gabata, kotunan kasar sun yanke hukuncin cewa tura 'yan sandan zuwa Haiti  ya sabawa doka.