1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'iLibiya

Kasashen EU sun aika tallafi Libiya

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 13, 2023

Gwamnatin Birtaniya ta bayyana daukin farko da za ta kai Libiya da aka kiyasta zai kai Fam miliyan daya, domin bayar da agajin gaggawa ga wandanda ibtila'in ambaliyar ruwa na birnin Derna ya rutsa da su.

https://p.dw.com/p/4WIz0
Libiya | Derna | Ambaliyar Ruwa | Agaji
Mummunar ambaliyar ruwa, ta janyo asarar rayuka a LibiyaHoto: Anadolu Agency/picture alliance

Birtaniyan ta ce tana aiki tare da abokanta da ke Libiyan, domin gano bukatun gaggawa da ake da sau da suka hadar da matsugunai da kayan kiwon lafiya da kuma na tsafta. Ita ma kungiyar Tarayyar Turai EU ta sanar da cewa kasashe mambobinta da suka hadar da Jamus da Romaniya da Finland sun aika da kayan agaji, bayan ibtila'in ambaliyar ruwan da ya afku a Libiyan da ya halaka sama da mutane dubu biyu da 300 yayin da dubbai suka bace.