Takun saka tsakanin Aljeriya da Mali
December 21, 2023Talla
Hukumomin Malinsun ce jakadin na Aljeriya ya tattauna da wakilan kungiyoyin 'yan tawayen Abzinawa ba tare da saninsu ba. Aljeriya dai na shiga tsakani don dawo da zaman lafiya a arewacin Mali bayan wata yarjejeniya da aka rattabawa hannu a shekara ta 2015 tsakanin gwamnatin Mali da kungiyoyin masu dauke da makamai na Abzinawa wacce aka sanni da yarjejeniyar Algers.Tun a karshen watan Agustan da ya gabata , tashin hankali ya barke a arewacin Malin tsakanin dakarun gwamnati da na kungiyar yan tawayen abzinawa bayan shafe shekaru takwas na kwanciyar hankali.