1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin tabbas kan mace-mace a Najereiya

Lateefa Mustapha Ja'afar
April 30, 2020

A Najeriya an shiga halin rudani, bayan da aka rinka samun mace-mace masu tarin yawa a jihar Kano, a daidai lokacin da ake fama da annobar Coronavirus. Hakan ya sanya gwamnatin tarayya kafa dokar zaman gida a jihar.

https://p.dw.com/p/3bd8y
Tricycles
Yawn mace-mace a Kano, ya sanya gwamnatin Tarayya saka dokar zaman gida a jiharHoto: DW/N. Zango

Cikin makonni baya-bayan nan, rahotanni sun cika kafofin yada labarai da na sada zumunta na zamani, kan yadda ake fama da mace-macen da ba a san dalilin afkuwarsu ba a jihar Kano da ke Trayarra Najeriya. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka samu matsala wakjen yin gwajin annobar Coronavirus a jihar, abin da ya tilasta rufe dakin gwajin cutar.

Wannan halin da Kano ta tsinci kanta dai, ya tilastawa shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari daukar matakin sanya dokar zaman gida ta makonni biyu a jihar. Dama dai ita ma gwamnatin jihar ta dauki matakin sanya dokar zaman gidan, gabanin ta'azzarar mace-macen.

Kwatsam kuma sai rahoton irin wadannan mace-mace ya bulla a takwararta jihar Borno, da ita ma ke yankin arewacin kasar, inda nan ma fitattun mutane suka rasa rayukansu cikin wannan makon, baya ga sauran mutanen gari da ake samun rahoton rasuwarsu ba tare da sanin musabbabi ba.