1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mafita kan rashin tsaro a kasashen Sahel

Abdullahi Tanko Bala
October 4, 2024

Babban taron Abuja kan matsalar tasaro a yankin Sahel ya ce dole kasashen su hada kai domin fuskantar kalubalen ta'addanci da ke barazana ga dorewar zaman lafiya a yankin

https://p.dw.com/p/4lQAO
Taron shugabannn kasashen ECOWAS
Taron shugabannn kasashen ECOWASHoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

Jiga-jigai a fanin tsaro da kwararu da ma shugabanin alumma suka hallara a Abuja wajen taro kan rashin tsaro a kasashen yankin Sahel inda aka duba halin da ake ciki na ayyukan ta'adanci a yankin da kuma kalubalen da ke fuskanta a Najeriya a yanzu. Janar Abdusslami Abubakar tsohon shugaban Najeriya ya nuna takaici da halin da Najeriyar ke ciki tare da bukatar hada kai da kasashen Sahel domin a yaki ta'addanci.

Karin Bayani: Kasashen Sahel biyar na atisayen soji a Jamhuriyar Nijar

Taron Ecowas a Abuja Najeriya
Hoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

An dai maida hankali ne a kan dalilan da ke sanya mutane shiga ta'adanci da ke zama sabuwar dabi'a a tsakanin alumma musamman matasa, matsalar da ke haifar da koma baya a fannoni da dama a yankin na Sahel. Mohammed Ibn Chambas shine shugaban kwamitin musamman na kungiyar tarayyar Afrika kan kasar Sudan kuma wakilin kungiyar kan shirin kawar da kananan makamai da ke hadasa yake-yake a Afirka. Ko yana ganin taro irin wannan zai yi wani tasiri a yanzu?

Karin Bayani: Juyin mulki bai hana rashin tsaron Sahel ba

Yace kwarai kuwa, wannan taro ne da kamfanin dillancin labaru na Najeriya ya shirya wanda shine babba a nahiyar Afrika, don haka kwararru da yan boko da manyan hafsoshin tsaro sun gano dalilai da ke haifar da halayyar ta'adanci, kuma ba dalili guda daya bane, akwai na cikin kasashenmu kamar na rashin gwamnati mai karfi da suka hada da rundunar soja wasu kasashen Sahel na da dazuzzuka da babu hukuma a wurin wannan ya bai wa yan ta'adda dama su saki jiki. Akwai dalilai na kasashen waje, dubi yadda wasu 'yan ta'adda ke shigowa ta Libya. Don haka an gano su wanene da kuma matakan da ya kamata a dauka a fattakesu a Najeriya da ma kasashen Sahel''.

Karin Bayani: Rikicin yankin Sahen ya raba daruruwan yara da matsugunansu

Yaki da mayakan Jihadi a Sahel
Yaki da mayakan Jihadi a SahelHoto: Inside the Resistance

Akwai wakilan kungiyar alummar yankin Afrika ta Yamma watau Ecowas da suka jaddada bukatar hadin kai domin duka kasashen yankin Sahel din na kokari a kan batu guda ne. Janar Christopher Musa shine babban hafsan tsaron Najeriya da ya bayyana abinda ke daga masu hankali.

Dr Dikko Radda shine gwamnan jihar Katsina daya daga cikin jihohin da ta fi fuskantar matsalar tsaro a yanzu ya ce matsalar tafi karfin amfani da kafin bindiga.

Karin Bayani: Yunkurin dakile 'yan ta'adda a Sahel

Kwararru na baiyana fatan dorewar nasarorin da aka fara gani a 'yan watanin nan ta hanyar wannan hadin kai da kasashen yankin Sahel din suka yi duk da sauyin mulki soja da wasu daga cikinsu ke ciki.